Home Back

CBN Ya Yi Alkawarin Kawo Karshen Hauhawar Farashin Kayan Masarufi

leadership.ng 2024/6/18
CBN Ya Yi Alkawarin Kawo Karshen Hauhawar Farashin Kayan Masarufi

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa, shi da sauran mambobin kwamitin tsara tattalin arzikin kasa za su yi duk mai yiwuwa na ganin an kawo karshen yadda farashin kayayyaki ke hauhawa a kasar nan.

Matakan CBN a kan wannan matsalar a bayyana yake, tun da kwamitin ya yi taronsa na farko a watan Fabrairu, inda kwamitin ya dauki matakin rage ruwan na cin bashi zuwa 400 daga kashi 22.75 per.

Gwamnan CBN, Cardoso ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da jaridar Financial Times, ya kuma kara da cewa, ba za a kara kudin ruwa ba har sai an shawo kan hauhawar farashi.

Ya kuma jaddada cewa, kwamitinsu zai ta yi dukkan abin da ya kamata na ganin an shawo kan hauhawar farashi wanda shi ne ya jefa al’umma cikin matsalar tsadar rayuwar da ake fuskanta.

Taro na gaba na kwamitin zai kasance ne a ranar 20 zuwa 21 ga watan Mayu 2024.

A kan yadda darajar naira ke fadi tashi, Cardoso ya bayyana cewa, da yawa daga cikin masu zuba jari da ake gani za su fice daga kasa a halin yanzu sun gamsu da yadda tattalin arzikin Nijeriya ke tafiya sun kuma shirya ci gaba da bayar da gudummawarsu wajen ganin an shawo kan matsalar da tattalin arzikin da ake fuskanta.

Ya kuma bayyana shirin CBN na dawo da amfani da tsare-tsaren tattalin arziki da aka yi watsi da su a shekarun baya, ya ce, dole mu dawo da tsarin da muke amfani da su shekara da shekaru, musamman ganin yadda aka amfana da su a wancan lokacin, in ji shi.

People are also reading