Home Back

RUƊANIN SIYASAR KANO: Gwamna Abba, magoya bayan Sarki da cincirindon ‘yan Kwankwasiyya sun kwana tsaron Fadar Sarki Muhammadu Sanusi II

premiumtimesng.com 2024/7/2
RUƊANIN SIYASAR KANO: Gwamna Abba, magoya bayan Sarki da cincirindon ‘yan Kwankwasiyya sun kwana tsaron Fadar Sarki Muhammadu Sanusi II

Cincirindon magoya bayan Sarki Muhammadu Sanusi II da dafifin ‘yan Kwankwasiyya sun yini sun kwana tsaron Gidan Sarki Muhammadu Sanusi II, har zuwa wayewar safiyar Lahadi.

Shi kan sa Gwamna Abba Kabir-Yusif da ya yini a gidan cur har zuwa dare, ya koma gidan daidai ƙarfe 1:17 na dare.

Dafifin tsare fadar ya biyon bayan zargin da ake yi cewa jami’an tsaro na jiran samun wata ‘yar dama domin su shiga da tuɓaɓɓen sarki, Aminu Ado a cikin gidan.

Dama tun da rana magoya bayan Aminu Ado ke cewa sai cikin dare za su shiga su fito da Sarki Muhammadu Sanusi II, ko da tsiya, kamar yadda aka yi masa bayan cire shi a 2020.

Cikin masu irin waɗannan zafafan kalaman har da tsohon Kwamishinan Ayyuka na zamanin mulkin Abdullahi Ganduje, wanda Ganduje ya cire bayan samun saɓani, wato Magaji.

Dama kuma gamayyar rundunar tsaro a Jihar Kano, sun ce umarnin kotu za su bi, ba umarnin Gwamna Abba ba.

Akwai alamomi da ke nuna cewa shi kan sa Aminu Ado ya na fakon samun damar a shiga da shi cikin gidan Sarki da tsakar dare.

Wakilin mu ya ci karo da wani bidiyo inda tsohon Sarki ke tsaye a cikin dandazon magoya bayan sa, ga wani tsaye kusa da shi ya na bayanin cewa jami’an tsaro sun kusa zuwa domin a danna Fadar A shigar da Aminu komin dare. Shi ma ya nuna cewa a can za su kwana zaman jiran a je a tafi da Aminu zuwa fada.

Ɗimbin jama’a sun riƙa kai gudummawar ruwa, lemo mai sanyi da abinci daban-daban ga dandazon jama’ar da suka kwana su na tsaron Fadar Sarki Muhammadu Sanusi II.

Alamomi da kalaman da ke yawo a cikin gari da soshiyal midiya na nuni da cewa za a ɗauki tsawon kwanaki ana tsaron fadar, kafin a shawo kan rikicin.

Yayin da ake wannan dambarwa, har yanzu dai Fadar Shugaban Ƙasa ba ta ce komai ba.

Tun a ranar Asabar dai tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya ce gwamnatin tarayya ta karya dokar ƙasa ta shiga cikin ruguguwar sha’anin mulkin Kano. Ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu ya guji haddasa fitina a Kano.

Haka Majilisar Malaman Jihar Kano ta yi kakkausan suka da kira ga Shugaba Tinubu cewa matsalar Kano ba ta gwamnatin tarayya ba ce, ta gwamnatin Kano ce. Ta ce kada ya bari wasu daga waje su haddasa fitina a Kano.

Kungiyar Lauyoyi ta Jihar Kano, NBA ta yi Allah wadai da yadda ake amfani da sojoji a ruɗanin sarautar Kano.

Idan ba a manta ba, shi ma Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam, ya ce Gwamnatin Tarayya ta karya dokar ƙasa, inda a cikin dare aka kai tsohon sarki Aminu Ado cikin Gidan Nasarawa, wanda mallakar Gwamnatin Kano ne, ba da sanin Gwamnan Kano ko neman iznin sa ba.

People are also reading