Home Back

Shugaban Mauritaniya ya sake lashe zabe

dw.com 4 days ago
Shugaba Mohamed Ould Cheikh El Ghazouani na kasar Mauritaniya
Shugaba Mohamed Ould Cheikh El Ghazouani na kasar Mauritaniya


Shugaba Mohamed Ould Cheikh El Ghazouani na kasar Mauritaniya ya lashe zaben shugaban kasra da aka gudanar inda ya samu sabon wa'adi inda ya samu kashi 56 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta tabbatar da wannan sakamakon a wannan Litinin. Shugaban ya taimaka wajen samar da zaman lafiya a kasar da ke ynakin Sahel inda ake samu tashe-tahsen hankula na kungiyoyin masu ikirarin jihadi.

Karin Bayani: Ana zaben shugaban kasa a Mauritaniya

'Yan takara bakwai suka fafata a zaben na ranar Asabar ta karshen makon da ya gabata, inda Shugaba  Mohamed Ould Cheikh El Ghazouani mai shekaru 67 da haihuwa ya samu sabon wa'adi na biyu na mulki na karin shekaru biyar kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ta Mauritaniya ya tanada.

People are also reading