Home Back

Wales na shirin ɗaukar Henry a matsayin kocin tawagarta

bbc.com 2024/10/6

Asalin hoton, Getty Images

Thierry Henry
Bayanan hoto, Thierry Henry ne kocin tawagar Faransa 'yan ƙasa da shekara 21

Mintuna 2 da suka wuce

Tsohon haziƙin ɗan wasan Arsenal da Faransa Thierry Henry na cikin mutanen da hukumar ƙwallon ƙafa ta Wales ke duba yiwuwar ɗauka a matsayin kocinta domin maye gurbin Rob Page.

Henry wanda tsohon mai horarwa ne a Monaco da Mntreal Impact, yanzu haka shi ne kocin tawagar Faransa 'yan ƙasa da shekara 21 kuma yana shirin jagorantar ta zuwa gasar Olympics da ƙasar za ta karɓi baƙunci.

Tsohon ɗan wasan gaban mai shekara 46 na da alaƙa da hukumar ƙwallon Wales Football Association of Wales (FAW) sakamakon yin aiki tare da su lokacin da yake koyon aikin zama koci.

FAW ta kori mai horarwa Page ranar Juma'a da ta wuce bayan ya shafe shekara uku da rabi a muƙamin sakamakon gaza samun gurbin zuwa gasar Euro 2024.

Wasu daga cikin shugabannin FAW na son kawo shahararren koci kamar yadda suka yi lokacin da suka naɗa tsohon ɗan wasan Manchester United Ryan Giggs a 2018.

Sai dai FAW ba za ta iya biyan Henry wani albashi mai tsoka ba idan aka kwatanta da wasu ƙasashe, amma saboda zai iya ci gaba da riƙe matsayinsa a ɓangaren mai sharhin wasanni a talabijin, suna ganin hakan ba zai hana su ɗauke shi ba.

Ana ganin hukumar ba za ta yi gaggawa ba wajen ɗaukar sa saboda Wales ba ta da wani wasa har sai watan Satumba; lokacin da za ta fafata da Turkiyya a wasan gasar Nations League.

People are also reading