Home Back

Yajin Aiki: ’Yan Ƙwadago Sun Dura Ginin Majalisar Tarayya, Sun Katse Wuta da Ruwa

legit.ng 2024/10/5
  • Kungiyar kwadago ta rufe majalisar dokokin kasar tare da katse ruwa da wuta na ginin a yajin aikin da 'yan kwadagon suka fara
  • An ruwaito kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya (PASAN), ta rufe kofar shiga ginin da wasu motocin bas guda biyu
  • Yajin aikin kungiyoyin kwadago na Najeriya NLC da TUC na ci gaba da daukar zafi a babban birnin tarayya Abuja

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Mambobin kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya (PASAN), reshen kungiyar NLC, sun rufe majalisar dokokin kasar, a yajin aikin da 'yan kwadagon suka fara.

A safiyar yau muka ruwaito yajin aikin kungiyoyin kwadago na Najeriya NLC da TUC na ci gaba da daukar zafi a babban birnin tarayya Abuja.

'Yan kwadago sun dura ginin majalisar dattawa da na wakilai
Yajin aiki: ’Yan kwadago sun datse ruwa da wuta na ginin majalisar tarayya. Hoto: @Imranmuhdz Asali: Twitter

Wakilin jaridar Daily Trust da ya je majalisar dokokin kasar domin duba halin da ake ciki ya taras PASAN ta rufe kofar shiga ginin da wasu manyan motocin bas guda biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yan kwadago sun gana da 'yan majalisa

Kungiyoyin kwadago dai sun tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani a yau bayan kin amincewar da gwamnatin tarayya na kara mafi karancin albashi zuwa sama da N60,000.

'Yan kwadagon ma su neman N494,000 sun yi wata ganawa da shugabannin majalisar dokokin kasar da manyan jami’an gwamnati a jiya Lahadi kan shiga yajin aikin.

Sai dai taron ya tashi ba tare da an samu wata nasara ba bayan da shugabanin kungiyoyin kwadagon sun ce babu gudu babu ja da baya kan shiga yajin aiki.

'Yan kwadago sun rufe ma'aikatun tarayya

An ce kungiyar kwadago ta datse wutar lantarki da ruwan sha ga wasu gine-ginen majalisar dattawa da na wakilai.

Mun ruwaito cewa kungiyoyin kwadago sun rufe babbar kofar ma'aikatar babban birnin tarayya Abuja wadda aka fi sani da kofar Minista a Abuja.

NLC ta rufe tashar wutar lantarki ta kasa

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar kula da rarraba wutar lantarki ta Najeriya (TCN) ta ce kungiyar ma’aikatanta ta rufe tashar wutar lantarki ta kasa.

Babban manajan hulda da jama’a na TCN, Ndidi Mbah, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya Litinin.ya ce lamarin da ya haifar da katsewar wuta a fadin kasar.

Asali: Legit.ng

People are also reading