Home Back

RIKICIN GWAMNATI DA DAILY TRUST KAN YARJEJENIYAR SAMOA: Abubuwan da ya kamata a sani game da Hukumar Sauraren Ƙorafe-ƙorafe Kan Kafafen Yaɗa Labarai (NMCC)

premiumtimesng.com 2024/8/19
‘Matsayar Mu Kan Rahoton Yarjejeniyar Samoa’ – Daily Trust

A ƙoƙarin ƙarfafa wa jama’a yarda da gaskata jaridu da sauran kafafen yaɗa labarai, an kafafen sun kafa wa kan su kwamiti ko hukuma wadda za ta riƙa sauraren ƙorafe-ƙorafe kan su, wato National Media Complaints Commission (NMCC), mai mambobi 9, wadda aka fi sani da National Ombudsman.

Hukumar ta na sauraren ƙorafe-ƙorafe ne kan wuraren da wasu jaridu suka buga labaran da ba sahihai ba, da sauran labaran da ba a bi ƙa’da wajen yaɗa su ko buga su ba.

Haka kuma aikin hukumar ce tabbatar da kare haƙƙin ‘yan jarida da haƙƙin ba su damar bayanan da suka wajaba su sanar wa jama’a.

An kafa hukumar cikin watan Afrilu, 2023.

A ranar Laraba ce wannan hukuma ta fuskanci gagarimin aikin ta na farko, yayin da Gwamnatin Tarayya ta rubuta wa hukumar wasiƙar ƙorafi dangane da labarin da Daily Trust ta buga kan Yarjejeniyar Samoa, wanda bai yi wa gwamnati daɗi ba.

“Mun kai ƙarar Daily Trust ga Hukumar Sauraren Ƙorafe-ƙorafen Jama’a kan Kafafen Yaɗa Labarai. Mun bayar da misalan wuraren da Daily Trust ta aikata ba daidai ba,” cewar Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris.

“Gwamnati na so Daily Trust ta fito ta wanke kan ta, idan kuma ta aikata ba daidai ba, to ta nemi afuwa ga ‘yan Najeriya da kuma gwamnati.

“Ai ba gazawa ba ce idan wanda ya yi laifi ya amsa laifin sa, kuma ya nemi afuwa. To idan aka yi haka, sai a wuce wurin kawai. Amma kada a yi tsammanin za mu harɗe ƙafafu mu yi shiru, ya yin da wata jarida ta buga labarin ƙarya wanda kuma bai wa ƙasar nan daɗi ba. Kuma sannan ta ƙi janye labarin. Akwai buƙatar a ɗauki hukunci. Dalili kenan muka kai ƙorafin mu ga Hukumar Sauraren Ƙorafe-ƙorafen Jama’a kan Kafafen Yaɗa Labarai,” cewar Idris.

Idris ya ce ya na so hukumar wadda a Turance ake kira ‘Ombudsman’ ta yi dubi da nazarin lamarin a tsanake, kuma da gaskiya.

Mamba na hukumar mai suna Lanre Idowu, ya ce idan hukumar ta samu wata jarida ta buga labarin da ba gaskiya ba ne, kuma aka kai masu ƙorafi, to za su umarci jaridar ta buga hukuncin da suka ɗauka cikin kwanaki bakwai bayan yanke hukunci.

Ƙungiyar Masu Wallafa Jaridu ta Najeriya na cikin hukumar (NPAN). Kuma ana bukatar kowace jarida ta buga labarin hukuncin da aka yi wa jaridar da aka samu da aikata ba daidai ba, a cikin kwanaki 14.

Mambobin Hukumar Sauraren Ƙorafe-ƙorafen Jama’a Kan Kafafen Yaɗa Labarai:

Shugaba: Emeka Izeze, tsohon Babban Daraktan jaridar Guardian.

Sauran sun haɗa da A. B Mahmood, (SAN), Chinyere Okunna, Hussaini Abdu, Lanre Idowu, Edetan Ojo, Dupe Ajayi-Gbadebo, Eugenia Abu.

People are also reading