Home Back

DAMBARWAR MASARAUTAR KANO: Kotun Tarayya a Kano ta ɗage sauraren ƙara zuwa ranar 13 ga Yuni

premiumtimesng.com 2024/6/30
SARAKUNA BIYU: Yayin da jami’an tsaro na musamman daga Abuja ke gadin Sarki Bayero, ƴan farauta ke gadin Sarki Sanusi

A daidai ƙarfe 2:35 na rana ne Mai Shari’a a Babbar Kotun Tarayya da ke Gyaɗi-gyaɗi, kan titin ‘Court Road’ ta ɗage sauraren ƙarar da dambawar masarautar Kano, zuwa ranar 13 ga Yuni.

Kotun ta ce a koma ranar 13 ga Yuni domin ta tabbatar shin ta na da hurumin sauraren ƙarar da tsigaggen Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba Ɗan’Agundi ya shigar, wadda ya ƙalubalanci rushe masarautar Kano, lamarin da ya shafi har da rawanin sa.

Gidan Radiyon Dala F.M da ke Kano ya ruwaito cewa Babbar Kotun Tarayya mai zaman ta a Gyaɗi-gyaɗi, Kano, ƙarƙashin Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman, ta ɗage zaman da ta fara na sauraron shari’ar da Aminu Babba Ɗan Agundi ya shigar, inda ya ke ƙalubalantar Gwamnatin Jihar Kano akan batun kwaskwarimar da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi wa dokar masarautu.

A zaman kotun na yau Alhamis, lauyan waɗanda aka yi ƙara, Barista Mahamud Abubakar Magaji, ya bayyana wa kotun cewar, a zaman yau za a tattauna ne kawai akan batun hurumin kotun akan wannan shari’ar.
Sai dai lauyan mai ƙara, Barista Waziri ya shaida wa kotun cewar ba su rubuta martanin su akan wannan batu ba. A nan kotun ta umarce su da su rubuto martanin su cikin da awa ɗaya.

Tun da fari dai Aminu Babba Ɗan Agundi ne ya shigar da ƙarar gwamnatin Kano da Majalisar Dokoki, sakamakon gyaran fuska da majalisar ta yi wa Dokar Masarautun Jihar Kano ta 2019, inda sabuwar dokar ta rushe masarautu biyar da aka ƙirƙira kuma daga bisani Gwamnan Kano, Abba Kabir-Yusuf ya sanya hannu, tare da bayyana Muhammadu Sunusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.

Rahotanni sun nuna cewa, yayin zaman, an girke jami’an tsaron ‘yan sanda da na DSS, wanɗanda suka hana shiga harabar Babbar Kotun Tarayya da ke Kano.

Jami’an tsaron sun kuma hana kowa shiga harabar kotun, sai iya waɗanda suke da hurumi a shari’ar da ‘yan jarida.

People are also reading