Home Back

Gobara ta kashe akalla mutum 10 a Brazil

dw.com 2024/5/7

Akalla mutum goma ne suka mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a wani rusashshen ginin otel da aka mayar tantuna ga wadanda ba su da matsugunni a birnin Porto Alegre da ke kudancin Brazil.

An ceto wasu tara sannan an kai su asibitoci da ke yankin domin karbar jinya.

Ma'aikatan bayar da agajin gaggawa sun tabbatar da mutuwar mutanen 10 yayin da wasu tara kuwa ke karbar jinya a sibitoci mafi kusa.

Gwamnan jihar Eduardo Leite dai ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan mamatan a shafinsa na X, tare da bayyana cewa ya kadu matuka da wannan ibtila’i.

Rahotanni sun nuna tantunan na wucin gadi an kafa su ne ba tare da sahalewar mahukunta ba.  

Tuni gwamnan jihar Eduardo Leite ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan mamatan a shafinsa na X, tare da bayyana cewa ya kadu matuka da afkuwar wannan ibtila'i.
 

People are also reading