Home Back

Kotun Koli Ta Tanadi Hukunci a Shari'ar da Tinubu Ya Kai Gwamnoni 36 Gaban Alkali

legit.ng 2024/7/5
  • Kotu ta dauki mataki game da shari'ar da ake yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da kuma gwamnonin jihohi 36 a Najeriya
  • Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar inda ta bukaci duka bangarorin su saurari ranar da za ta tuntube su
  • Wannan na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya ta maka gwamnoni a gaban kotu kan dakile ƴancin ƙananan hukumomi a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar Gwamnatin Tarayya da gwamnonin jihohi 36.

Kotun ta dauki matakin ne a yau Alhamis 13 ga watan Yuni kan korafin da aka shigar da gwamnonin kan ƴancin ƙananan hukumomi a kasar.

Mai Shari'a, Mohammed Lawal Garba wanda ya jagoranci alkalan guda bakwai ya ce za su byyana ranar yanke hukuncin karshe ga duka bangarorin, cewar The Nation.

Lawal Garba ya bayyana haka ne jim kadan bayan lauyoyin duka bangarorin sun gabatar da korafe-korafensu kan shari'ar.

Hakan ya biyo bayan maka gwamnoni 36 da ke Najeriya kan tauye hakkin kananan hukumomi 774 da suke yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani kotu ta ba gwamnoni 36 wa'adin mako daya da su yi martani kan zarginsu da ake yi.

Har ila yau, kotun ta umarci Ministan Shari'a ya yi martani cikin kwanaki biyu bayan karbar korafi daga gwamnonin.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading