Home Back

Amurka: Sarkin Leken Asiri Na Neman Habaka Karfinta

leadership.ng 2024/8/21
Amurka: Sarkin Leken Asiri Na Neman Habaka Karfinta

LTun daga shekarar 2023, hukumomin gwamnatin Amurka suke kirkiro labaran kanzon kurege, suna ikirarin wai kungiyar kutsen yanar gizo ta “Volt Typhoon” dake samun goyon bayan gwamnatin Sin, ta kai hare-hare kan yanar gizon muhimman manyan ababen more rayuwa na kasar, a yunkurin kara gishiri ga zargin da suke yi wa kasar Sin na wai “Sin na kawo barazana ga sauran kasashen duniya”. Lallai sarkin leken asiri na zargin wasu cewa, wai an kutsa cikin yanar gizonta, abin dariya ne.
Kwanan baya, sassan kula da tsaron yanar gizo na kasar Sin sun yin bincike har sun samar da karin bayani game da makarkashiyar da Amurka ta yi game da shirin “Volt Typhoon”, binciken da ta yi ya nuna cewa, hukumomin gwamnatin Amurka da wasu hukumomin tsaron yanar gizo na kasashen Amurka da Birtaniya da Canada da Austriliya da New Zealand wato “Five Eyes Alliance” sun yi hadin kai wajen kirkiro labaran karya. Abin da suka gabatar wai shi ne shaida game da shirin “Volt Typhoon”, ba ya da alaka da kasar Sin, daga wata kasa ta daban aka samo shi, amma Amurka ta zargi kasar Sin kan wannan abu cewa, wai shi ne shaida dake bayyana harin da Sin ta kaiwa yanar gizonta. Har ‘yan siyasar wadannan kasashe sun kirkiro labarin karya, da zummar shafawa kasar Sin bakin fenti wai tana kawo barazana ga tsaron yanar gizo. Da hakan, hukumar tsaron Amurka ta tsorata da yaudari majalisar dokokin kasar da ta tsawaita wa’adin aya mai lamba 702 na dokar sa ido kan leken asiri a ketare wato FISA, wanda aka fi sani da dokar leken asiri ba tare da samun izini daga kotu ba, da kuma neman karin kasafin kudade daga majalisar dokoki don inganta karfin kutse na hukumomin leken asiri na kasar.
‘Yan siyasar Amurka ba su gamsu da karfinta na leken asiri a yanzu ba, suna yunkurin leken asiri da sarrafa ra’ayin jama’a ta hanyar mai da fari baki da kirkirar labaran kanzon kurege, suna kan wata mahaukaciyar hanya ta leken asiri. (Mai zane da rubutu: MINA)

People are also reading