Home Back

Atiku Abubakar Ya Faɗi Dalilin da Zai Sa Ya Goyi Bayan Peter Obi a Zaben 2027

legit.ng 2024/6/26
  • Atiku Abubakar ya ce zai marawa Peter Obi ba tare da shakkar komai ba idan PDP ta tsayar da shi takarar shugaban ƙasa a 2027
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ba zai yi jayayya da jam'iyyar PDP matuƙar ta zaɓi bai wa ɗan Kusu maso Gabas takara
  • Ya ce ko a zaɓen 2023 ya nemi takara ne saboda babbar jam'iyyar adawa ta buɗe kofa ga kowane mamba idan yana sha'awar takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Alhaji Atiku Abubakar ya ce zai marawa Peter Obu baya idan har jam'iyyar PDP ta yanke tsayar da shi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a 2023, ya ce ba abin da zai hana ya goyi bsyan Obi matuƙar jam'iyyar ta miƙa tikitin takara zuwa Kudu maso Gabas.

Obi tare da Atiku Abubakar.
Atiku ya tabbatar da cewa zai marawa Obi bayan idan PDP ta ba shi takara a 2027 Hoto: @Atiku Asali: Facebook

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi wannan furucin ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bayyana cewa ya shiga tseren neman tikitin takarar shugaban ƙasa a bara ne saboda PDP ta buɗe ƙofa ga kowane yankin Najeriya.

Jaridar Vanguard ta ruwaito Atiku na cewa:

"Na sha nanata cewa idan PDP ta yanke miƙa takara ga shiyyar Kudu maso Gabas ba zan nemi takara ba, ko a zaɓen 2023 na nanata wannan kalaman, matukar PDP da yanke zan yi mata ɗa'a.
"To amma na shiga takarar tikitin shugaban ƙasa ne saboda jam'iyya ta buɗe kofa ga kowane mamba. Idan jam'uyya ta ce yanzu lokacin Kudu maso Gabas ne kuma aka zaɓi Obi, zai mara masa baya."

Wazirin Adamawa ya ƙara da cewa akwai yiwuwar haɗa maja tsakanin PDP da jam'iyyar LP, yana mai cewa jam'iyyar PDP ce kaɗai za ta yanke makomarsa a siyasa.

Atiku ya ce ganawar da ya yi da Peter Obi kwanan nan wata alama ce da ke nuna akwai yiwuwar za su haɗa kansu gabanin babban zaɓen 2027.

Magoya bayan APC sun soki masu shirin maja

A wani rahoton kuma Ƙungiyar NPH mai goyon bayan APC ta mayar da martani kan yunkurin ƴan adawa na haɗa maja gabanin zaɓen 2027.

Shugaban NPH, Hon. Bukie Okangbe ya ce babu wani kawance da ƴan siyasa za su ƙulla wanda zai kawo ƙarshen mulkin APC a zaɓe na gaba.

Asali: Legit.ng

People are also reading