Dakarun Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Ta'adda, Sun Hallaka Mutum 2 a Kaduna
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta da ke yaƙi da ta'addanci a jihar Kaduna, sun yi nasarar daƙile wani harin ƴan ta'adda.
Rundunar ta ce dakarun sun kuma yi nasarar hallaka ƴan ta'adda mutum biyu bayan sun yi musu kwanton ɓauna.
Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da rundunar sojojin Najeriya ta sanya a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta bayyana cewa sojojin bayan samun bayanin sirri sun yiwa ƴan ta'adda huɗu da ke kan babura kwanton ɓauna a Kurmin Aja, cikin ƙaramar hukumar Kagarko yayin da suke kan hanyar kai hari.
Dakarun sojojin sun yi musayar wuta da ƴan ta'addan tare da hallaka biyu daga cikinsu yayin da sauran suka tsere ɗauke da raunukan bindiga zuwa cikin daji.
Bayan artabun da ƴan ta'addan, sojojin sun kuma ƙwato makaman da suka haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda biyu, harsasai guda 30 masu kaurin 7.62mm, jigida guda uku da babura guda biyu.
Rundunar sojojin ta shawarci mutanen yankin da su kasance masu sanya ido kan abubuwan da ke faruwa, su ci gaba da gudanar harkokinsu na yau da kullum tare da kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba ga jami'an tsaro.
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun runduna ta ɗaya ta sojojin Najeriya da ke aiki a Kaduna sun kashe ƴan ta'adda bakwai a ƙauyen Udawa da ke ƙaramar hukumar Chikun a jihar.
Dakarun sojojin sun samu nasarar ne a wani aikin sintiri da suka gudanar a kan hanyar Udawa-Kurebe a ranar Lahadi, 19 ga watan Mayun 2024.
Asali: Legit.ng