Home Back

Hajjin 2024: Gwamna Yusuf ya biya N376m cikon kuɗin BTA na maniyyatan Kano sanadiyyar tashin farashin Dala

premiumtimesng.com 2024/6/26
Ƴan Adawa su jira su ga irin abinda zan yi wa Kanawa a cikin wa’adin mulki na tukunna – Gwamna Yusuf

Gwamnan Kano, Abba Yusuf ya ce gwamnatin za ta yi wa kowanne maniyyaci daga jihar cikin naira Naira 121,000 kuɗin guzirinsa wanda aka samu matsalar rashin kaiwa Dala 500 saboda tashin farashin Dala a kasuwan canji.

Kuɗin da gwamnati zata biya dai ya tashi akan Naira miliyan N376,310,000.

Idan dai ba a manta ba a kwanakin baya ne hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta sanar da cewa za a ba wa maniyyatan aikin hajjin bana dala 500 kowannensu a matsayin BTA.

Amma kuma saboda tashin farashin dala a kasuwan canji sai kuɗin ya yi kasa da da abinda aka shirya baiwa Alhazan.

Dalilin Haka ne gwamna Abba Yusuf ya yi kukan kura ya cika wa dukan maniyyatan jihar rarar da aka samu.

Dukkan su yanzu kowa zai zamu dala 500 kamar yadda aka tsara.

Bayan haka kuma gwamna Yusuf ya ce mataimakin gwamnan jihar Aminu Abdulsalam ne zai jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa akasa mai tsarki, yana mai cewa mataimakin gwamna zai baiwa Alhazan jihar Kyakkyawar kula a lokacin aikin Haji.

A karshe ya yaba wa hukumar Alhazai ta kasa bisa kokarin da ta ke yi na tabbatar da an samu nasarar aikin a bana.