Home Back

Babban Jami'in Hukumar Kwastam Ya Mutu a Cikin Majalisar Tarayya, Bayanai Sun Fito

legit.ng 2024/7/2
  • An tafka babban rashi bayan mutuwar wani babban jami'an hukumar Kwastam a cikin Majalisar Tarayya a Abuja
  • Marigayin ya rasu ne bayan ya fadi kasa yayin da mambobin kwamitin Majalisar kan binciken kudi ke yi masa tambayoyi
  • An kwashi Essien Etop Andrew zuwa asibiti bayan ya yi tari ya fadi inda aka tabbatar da mutuwarsa a can

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Wani babban jami'in hukumar Kwastam ya riga mu gidan gaskiya a Majalisar Tarayya da ke Abuja.

Marigayin mai suna Essien Etop Andrew ya rasu ne yayin da yake amsa tambayoyi daga mambobin Majalisar.

Kafin rasuwarsa, Andrew shi ne mataimakin kwanturola a bangaren gudanar kudi na hukumar da ke Abuja, cewar TheCable.

Jim kadan bayan faduwarsa, an kwashi Andrew zuwa asibiti inda aka tabbatar da rasu nan take.

Kafin faduwarsa, an tabbatar da cewa sai da Andrew ya yi tari kafin ya kife kasa cikin Majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karin bayani na tafe.....

Asali: Legit.ng

People are also reading