Home Back

Me zai faru idan Donald Trump ya lashe zaɓen shugaban Amurka?

bbc.com 6 days ago
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya buɗe hannayensa a yayin da yake gabatar da jawabi a Florida a cikin watan Yunin 2024

Asalin hoton, Getty Images

Ƙuri'ar jin ra'ayi ta nuna cewa tsohon shugaba Donald Trump na iya nasara a karo na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na watan Nuwamba, amma dai ya yi wuri a yanke hukunci.

Duk wanda ya yi nasara, sakamakon zai girgiza duniya - tare da tasiri a rayuwar miliyoyin mutane a ciki da wajen Amurka.

Trump - wanda ake gab da tabbatar da shi a matsayin dan takarar shugabanci kasa a inuwar jam'iyyar Republican a taronsu na kasa da za a gudanar a watan Yuli - bai fiya bayyana cikakken bayani a kan shirinsa ba.

Amma a bayyane take cewa akwai wurare da dama da tsare-tsarensa za su iya sanya ya dusashe hasken shugaba Joe Biden. Ga wasu daga cikinsu.

Ko Trump zai ci gaba da taimaka wa Ukraine?

US President Joe Biden (right) greets Ukrainian President Volodymyr Zelensky at the June 2024 G7 summit in France

Asalin hoton, Getty Images

Donald Trump ya jima yana suka kan maƙudan biliyoyin kuɗaɗen da Amurka ke kashewa wajen taimakon soji a Ukraine tun fara mamayar da Rasha ke yi a Ukraine a 2022.

Trump, wanda ke fitowa karara yana yabon Shugaba Putin a lokacin mulkinsa, ya alkawarta kawo karshen yakin cikin sa'o'i 24 idan aka zabe shi. Bai bayyana hanyar da zai bi ba, amma kalamansa sun ja hankali da damuwa kan makomar Ukraine.

Ɗaya daga cikin makusantansa, Firaministan Hungary Viktor Orban, ya ce Trump "ba zai bayar da ko sisi ba" ga Ukraine idan aka zabe shi, bayan ziyarar da ya kai wa tsohon shugaban a Florida a watan Maris.

Zabtare kuɗaɗen da ake kashewa na taimakon soji ya yi daidai da ra'ayin masu zabe 'yan Republican. Wata kuri'a ta jin ra'ayi da aka wallafa a ranar 8 ga watan Mayu ta cibiyar Pew Research, kashi 49 cikin 100 na 'yan Republican sun ce Washington na kashe kudade da yawa a kan Ukraine, idan aka kwatanta da kashi 17 cikin 100 na masu zaben Democrats.

Ko Trump zai janye Amurka daga Nato?

Kungiyar tsaro ta Nato mai kasashe 32 da suka hada da Amurka da Burtaniya da Jamus da Faransa na daya daga cikin kasashen da ke nuna kiyayya da Trump.

A matsayin shugaban kasa, ya sha barazanar janye Amurka daga cikin kungiyar idan suka gagara cimma yarjejeniyar kashi biyu cikin 100 na kudaden shigarsu.

A karkashin dokar Nato, duk wani hari a kan mamba guda na kungiyar tamkar hari ne ga kungiyar baki daya.

Amma a watan Fabarairun wannan shekarar Trump ya ce ba zai kare kasar da ba ya biyansu ba kuma zai ci gaba da karfafawa Moscow.

American (left) and Nato flags are seen flying together in Warsaw on 12 April 2024

Asalin hoton, Getty Images

Ana ci gaba da samun mabanbanta ra'ayi kan ko zai janye alakar Amurka da ƙawayenta.

Amma Ed Arnold daga cibiyar bincike ta Landan ya ce yana iya yi wa aikin nasu zagon kasa ba tare da ja fidda Amurka ba, ta hanyar kara yawan sojojin Amurka a Turai a kuma kakaba dokoki mai tsauri kan batun Rasha da Ukraine.

Trump ya sha alwashin tasa ƙeyar baƙi

Shugabancin Trump na tattare da ce-ce-ku-ce kan tsare-tsarensa na baki, kuma ya alkawarta sake tsawwala yanayi da zarar ya hau mulki.

Ya ce a wata rana zai aiwatar da gagarumin shirin mayar da kowane bako gida domin kafa tarihi a Amurka.

A group of migrants wait in line near a US Border Patrol field processing centre after crossing the Rio Grande from Mexico on 18 December 2023 in Texas

Asalin hoton, Getty Images

Jam'iyyar Republican ta alkawarta kawo karshen tsarin zama dan kasa ta hanyar haihuwa ga yaran da iyayensu ba 'yan kasa ba ne da kuma kaddamar da yaki kan kasurguman masu harkar kwaya a Mexico.

Kuma a shekarar da ta gabata, Trump ya ce zai fadada dokar haramcin bayar da biza musamman a kasashen da Musulmi ke da rinjaye.

Shafin Trump ya sanar da cewa lokacin da yake mulki ya dakatar da shirin bai wa 'yan gudun hijira dama a kasar, kuma yanzu ma idan ya hau mulki hakan zai dora a kai.

Sai dai akwai masu ganin tsohon shugaban zai fuskanci kalubale daga bangaren shari'a kan wannan shiri nasa, kamar yadda aka gani a lokacin mulkinsa na farko, inda kotuna suka rinka taka masa burki kan wasu dokoki irinsu haramcin tafiya.

Shugaba Biden ya alkawarta bijiro da tsare-tsare kan yan cirani masu sauki sannan ya dakatar da wasu shirye-shirye na zamanin mulkin Trump. Sai dai kuri'ar jin ra'ayi na ci gaba da nuna cewa akwai damuwa kan yadda ake tafiyar da harkokin baki a kasar.

Ko Trump zai ci gaba da mara wa Israel?

A lokacin mulkinsa, Trump gaba-gadi yake fitowa yana nuna cikakken goyon-baya ga Isra'ila da kuma gwamnatin masu ra'ayin rikau.

Ya sanar da matakin Amurka na ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin tarayyar Isra'ila, tare da watsi da tsare-tsaren Amurka na shekaru da dama, tare da dauke ofishin jakadancin Amurka daga Tel Aviv zuwa Kudus.

Wadannan matakai na Trump sun nuna karara goyon-bayan da yake nuna wa Isra'ila a kan Falasdinawa.

Ya nuna goyon baya ga mamayar Yahudawa a yankin gabar yamma da kogin Jordan - wanda kasahen yamma da dama ke ganin akwai rashin dacewa karkashin yarjejeniyar kasa da kasa, ko da yake Isra'ila ta nuna adawarta.

Gwamnatinsa ta kuma shiga tsakani wajen daidaita alaka tsakanin Isra'ila da kasashen Larabawa na Bharain da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa wato UAE da Sudan da Morocco.

Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu (left) and US President Donald Trump participate in the signing ceremony of the Abraham Accords between Israel and the UAE, and Israel and Bahrain, on the South Lawn of the White House on 15 September in Washington

Asalin hoton, Getty Images

Kodayake, akwai wadanda ke ganin an samu rashin jituwa tsakaninsa da Benjamin Netanyahu tun bayan zaben shugaban kasar Amurka ta 2020, lokacin da firaministan na Isra'ila ya kira Mista Biden domin taya shi murna yayinda Trump ke nuna adawarsa.

Cikin yanayi na hare-haren da aka kai a ranar 7 ga watan Oktoba, Trump ya ce Mista Netanyahu bai shiryawa harin Hamas ba tare da kiran Hezbollah a matsayin mayakan Lebanon, da ke assasa rikici ta hanyar tunzura 'yan Isra'ila da ke goyon bayan jam'iyyar Repubican.

Ya ci gaba da jadadda goyon bayan da ya jima yana nunawa Isra'ila, amma ya ce dole kasar ta karasa abin da ta soma a kan Hamas a Gaza.

Ya alakar Trump za ta kasance da China?

Former US President Donald Trump points at something at a press conference during his 2017 visit to Beijing

Asalin hoton, Getty Images

A lokacin da yake kan mulki, Trump ya haifar da zazzafan rikicin kasuwanci da China. Ya ce idan aka sake zaben sa, zai kakaba wa kasar harajin sama da kashi 60 cikin 100.

A bara ya yi wasu kalamai masu tsauri kan makomar China da yadda zai dakushe ta a kowanne fanni kama daga gine-gine da makamashi da sadarwa.

Yayin da ake ci gaba da fuskantar tashin hankali a kudancin China da kuma kan Taiwan, wasu na fatan ganin tsare-tsaren Amurka na tsaro sun mayar da hankali kan China.

Taiwan yanki ne mai cin gashin kai da ke ganin babu alaka tsakaninsu da China, saboda tana da kundin tsarin mulkinta da gudanar da zaben shugabanninta.

Sai dai Beijing na musu kallon wani yanki nata da ke bore kuma tana ganin za ta mayar da ita kan hanya.

Amurka karara ba ta fito ta bayyana yadda za ta yi ba ko mataki idan China ta mamaye Taiwan, kodayake Mista Biden a kullum kalmarsa ita ce Amurka za ta kare kanta.

Trump dai yaki ambata abin da zai yi. Sai da ya taba tunzura China a zaben 2016, lokacin da ya karbi sakon taya murna daga shugaban Taiwan.

Ina batun muhalli?

A matsayinsa na shugaban kasa, Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyara sauyin yanayi ta Paris ta 2015. Mista Biden ya sake waiwaye a kai - amma shafinsa na gangamin yakin neman zabe na cewa zai sake ficewa.

Sannan shafin ya ce zai hana wasu ayyukan danyen mai da ke gurbata muhalli irin su rage haraji ta fannin mai da iskar gas da gawayi da wasu tsare-tsare da Mista Biden ya bijiro da su.

 Emissions rise from a coal-fired power plant in the US state of West Virginia

Asalin hoton, Getty Images

Dr Simon Evans, mataimakin editan shafin da ke sa ido kan sauyin yanayi na Carbon Brief, ya ce da wuya Amurka ta cimma yarjejeniyar kasashen duniya kan sauyin yanayi da zarar Trump ya koma kan mulki.

Mista Biden ya zuba dala bilyan 300 wajen bunkasa da kawo sauyi a fanin makamashi mai tsafta da kawar da abubuwan da ke gurbata muhalli.

Sai dai akwai masu fafutukar kare muhalli da ke adawa da shirin, suna mai cewa ana dai sake habaka harkar danyen mai da iskar gas ne.

Ana ganin Biden na iya kokarinsa, a cewar Dr Simon.

People are also reading