Home Back

Abubuwan da suka kamata ku sani kan zaɓen shugaban ƙasar Chadi na 2024

bbc.com 2024/5/6

Asalin hoton, Getty Images

.
Bayanan hoto, Al'ummar Chadi za su fita rumfunan zaɓe ranar 6 ga watan Mayu

A ranar 6 ga watan Mayun 2024 ne al'ummar Chadi za su fita rumfunan zaɓe domin zaɓar sabon shugaban ƙasar.

Kawo yanzu 'yan takara 10 ne ke fafatawa don samun damar ɗarewa karagar mulkin ƙasar.

Tuni majalisar tsarin mulkin ƙasar ta wallafa sunayen 'yan takarar da suka nuna sha'awarsu ta tsayawa a zaɓen - wanda ke da muhimmanci ga ƙasar don zaɓar sabon shugaba tun bayan rasuwar Idriss Deby Itno a filin yaƙi.

Ɗansa Mahamat Idriss Deby - wanda ya gaje shi tun bayan rasuwar mahaifinsa nasa a watan Afrilun 2021 - na cikin 'yan takarar da za su faffata a zaɓen.

Babban mai hamayya da shi Succès Mastra, wanda firaministansa ne, shi ma na cikin waɗanda ke zawarcin kujerar shugabancin ƙasar.

Bayan miƙa takardunsu na nuna sha'awar tsayawa takara da aka gudanar daga ranar 6 zuwa 15 ga watan Maris, majalisar tsarin mulkin ƙasar ta karɓi takardun mutum 20 da suka nuna sha'awarsu.

Amma ta tantance mutum 10, bayan ta nuna rashin amincewarta da sauran, sakamakon rashin cika wasu ƙa'idojin tsayawa takarar dangane da takardunsu da sauran bayanai.

Daga cikin mutanen da majalisar tsarin mulkin ta yi watsi da buƙatar tasu har da manyan 'yan takarar hamayya biyu, Nassour Ibrahim Neguy Koursami, da Rakhis Ahmat Saleh saboda kasa cika wasu sharuɗɗa da majalisar ta gindaya.

Nassour Ibrahim Neguy Koursami na da matsalar “gudanar da bincike kansa game da batun zargin aikata laifin amfani da 'takardun boge", saboda zargin da ake yi masa na hadin baki game da sahihancin takardunsa na tsayawa takara.

Zaɓen shugaban ƙasa a lokacin matsi

Asalin hoton, Getty Images

..
Bayanan hoto, Mahamat Idriss Déby ne shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya

Matsalar ta samo asali ne tun bayan ƙarin farashin man fetur, ƙari kan matsalar yawan 'yan gudun hijira a ƙasar, lamarin da ya sa gwamnatin ƙasar ta ayyana dokar ta-ɓaci kan abinci da abinci mai gina jiki a ƙasar. Amma duk da haka masu bayar da tallafi ba sa taimaka wa ƙasar.

Hukumar Yaƙi da Yunwa ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan yara 480,000 ne ke fama da rashin abinci mai gina jiki a Chadi.

Sannan jerin zanga-zangar da ƙungiyoyin fararen hula ke shiryawa don nuna adawa da halin da ƙasar ke ciki, na fuskantar sokewa kowane lokaci daga gwammnatin ƙasar.

Mahamat Idriss Deby zai shiga zaɓen domin zama halastaccen shugaban ƙasar, idan ya samu nasara a zaɓen.

A ranar 10 ga watan Oktoban 2024 ne aka tsara miƙa mulki ga zaɓaɓɓiyar gwamnati a ƙasar.

Daga nan ne kuma ƙasar za ta joma ƙarƙashin halastacciyar gwamnati da al'umma suka zaɓa, kamar yadda Ahmet Barchiret shugaban hukumar da ke sanya idanu kan harkokin zaɓen ƙasar, ANGE ya bayyana.

Wannan lokaci ne na nuna buƙata ga 'yan takara, hakan ne ya sa zaɓen shugaban ƙasar ya zama mai matuƙar ƙalubale, inda wasu 'yan siyasar ƙasar, kamar Succès Mastra ke buƙatar ɗarewar kujerar shugabancin ƙasar.

Adadin masu kaɗa ƙuri'a a zaɓen

Zaɓen raba-gardama da aka gudanar a watan Disamban bara ne ya amince da zaɓen shuagaba ƙasar.

Hukumar ANGE ta nuna cewa kashi 63 cikin ɗari na al'ummar ƙasar ne suka shiga zaɓen raba gardamar da aka gudanar.

Idan aka yi la'akari da wannan adadi, kenan fiye da mutum miliyan takwas ne suka yi rajistar zaɓe, daga cikin al'ummar ƙasar miliyan 17.72.

Waɗannan mutane ne za su fita domin kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasar da ke tafe.

Hukumomin da ke shirya zaɓe a Chadi

Asalin hoton, Getty Images

.
Bayanan hoto, Mambobin majalisar tsarin mulkin Chadi

Majalisar tsarin mulkin ƙasar ce ke da ikon shirya zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokokin ƙasar, bayan tantance yadda zaɓen ke gudanar, haka kuma ita ce ke da alhakin ayyana wanda ya lashe zaɓen, bayan hukumar zaɓen ƙasar (CENI)ta aike mata da sakamakon zaɓen.

Majalisar tsarin mulkin ƙasar - ƙarƙashin jagorancin Jean-Bernard Padaré - na da mambobi tara ciki har da alƙalan majistare biyar.

Majalisar ce ke da alhakin tantance 'yan takara tare da wallafa sunayen mutanen da suka cancani tsayawa takara a zaɓen.

A zaɓen ƙasar da ya gabata, hukumar zaɓen ƙasar 'Independent National Electoral Commission' (CENI), ce ke da alhakin gudanar da harkokin zaɓen tare da fitar da sakamakon, to sai dai a watan Janairun da ya gabata ne aka mayar da wannan aiki ƙarƙashin hukumar kula da shirya zaɓen ƙasar, 'National Election Management Agency' (ANGE)

Saɓanin CENI, hukumar ANGE hukuma ce ta dindindin - wadda ke da mambobi 15 da aka zaɓo tsakanin manyan mutane bisa sharuɗan cancanta, da rashin nuna ɓangaranci, sannan suzama babu wanda ke juya su, kamar yadda dokar da ta kafa hukumar ta tanadar.

Akan naɗa mambobin hukumar na tsawon wa'adin shekara bakwai, tare da zaɓin tsawaita musu sau ɗaya, sannan kuma za su sha rantsuwa kafin fara aiki da hukumar.

Don haka aikin hukumar ANGE shi ne kula shirya zaɓen da tabbatar da sabunta takardun zaɓe, da kula da kayyakin gudanar da zaɓen da wallafa sunayen masu kaɗa ƙuri'a, kamar yadda dokar zaɓen ƙasar ta tanadar.

Dangane da zaɓen ƙananan hukumomi da na gundumomi kuwa, kotun ƙolin ƙasar ce ke da alhakin wallafa sakamakon zaɓen.

Wane ne ya cancanci kaɗa ƙuri'a a Chadi?

Sashe na uku na dokar zaɓen ƙasar ta yi tanadin cewa duk ɗan ƙasar mace ko namiji da ya kai shekara 18 zai iya kaɗa ƙuri'a.

Dole ne duk wanda ke son kaɗa ƙuri'a ya yi rajista da hukumar zaɓen ƙasar.

Haka kuma dokar ta yi tanadin cewa dole ne ya kasance ba shi da wani abu da zai sa doka ta hana shi wannan damar.

Yadda tsarin zaɓen yake

Zaɓen shugaban ƙasar Chadi na gudana ne bisa tsarin masu zaɓe su zaɓi ɗan takara guda, kuma wanda ke da rinjayen ƙuri'u ne ke yin nasara a zaɓen.

Ana zaɓar shugaban ƙasar ne bisa wa'adin shekara biyar, wanda kuma akan iya sake zaɓarsa sau ɗaya.

Ɗan takarar da ke da mafi rinjayen ƙuri'u a zagayen farko a zaɓen ne ke samun nasara a zaɓen.

Idan ba a samu wanda ke da mafi rinjayen ƙuri'u a zagayen farko ba, to sai a tafi zagaye na biyu da za a gudanar a Lahadi ta biyu daga ranar da aka gudanar da zagayen farko.

Za kuma a gudanar da zaɓen ne tsakanin manyan 'yan takara biyu da ke kan gaba a zagayen farko.

Inda kuma za a ayyana wanda ya samu mafi rinjayen ƙuri'u a zaɓen zagaye na biyun a matsayin wanda ya yi nasara.

Wane ne ya cancanci tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasar Chadi?

Asalin hoton, Getty Images

.
Bayanan hoto, Firaministan ƙasar Succès Masra, da ke samun goyon bayan ƙawancen jam'iyyun 'Justice and Equality', na daga cikin 'yan takara

Sashe na 148 na dokar zaɓen ƙasar ya yi tanadin cewa dole ne wanda ke son tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasar ya kasance:

  • Ya kasance ɗan Chadi ta hanyar haihuwa, dole ne mahaifisa ko mahaifiyarsa su kasance 'yan Chadi, kuma ba shi da takardar zama ɗan wata ƙasa in ba Chadi ba
  • Dole ne shekarunsa su kai aƙalla shekara 35
  • Ya zaman yana da 'yancin zama ɗan ƙasa da 'yancin shiga siyasa
  • Ya kasance yana da lafiyar jiki da ta kwakwalwa
  • Ya zama ya zauna a ƙasar na aƙalla shekara guda a cikin shekara uku da suka gabata
  • Ka zauna inda za a iya samunka idan ka kasance mamba a rundunar tsaron ƙasar (sashe na 149)
  • Dole ne ɗan takara ya ajiye saifa miliyan 10 a asusun ajiyar ƙasar, wanda za a dawo masa da shi, idan ya samu aƙalla kashi 10 na ƙuri'un da aka kaɗa (Sashe na 152)

'Yan takara a zaɓen shugaban ƙasar na ranar 6 ga watan Mayu

Asalin hoton, Getty Images

..
Bayanan hoto, Lydie Beassemda, 'yar takarar jam'iyyar PDI, ta kasance mace ɗaya tilo cikin jerin 'yan takarar 10

'Yan takjara sun miƙa takardunsu na snuna sha'awar tsayawa takara tsakanin 6 zuwa 15 ga watan Maris.

Bayan haka ne majalisar tsarin mulkin ƙasar ta yi wa mutum 20 rajistar tsaywa takara, inda ta tabbatar da 10 bayan tantancewa.

Shugaban riƙon ƙwaryar ƙasar, Mahamat Idriss Deby, na daga cikin 'yan takarar da aka tantance don shiga zaɓen, wanda ke samun goyon bayan ƙawancen jam'iyyu na 'Chad United coalition'.

Haka ma firaministan gwamnatinsa wanda ya daɗe yana hamayya da gwamnatin, Succès Mastra na daga cikin 'yan takarar da aka tantance, wanda shi ma ke samun goyon bayan ƙawancen jam'iyyun 'Justice and Equality coalition'.

Waɗannan su ne manyan 'yan takara da ake ganin fafatawar za ta fi safi tsakaninsu.

Haka ma akwai Lydie Beassemda, wadda mace ce a cikin jerin 'yan takarar. wanna shi ne karo na biyu da matar - wadda ke wakiltar mata a takarar shugabancin ƙasar - ke fafatwa a zaɓen shugaban ƙasar.

Misis Lydie - wadda ƙwararriya ce a fannin samar da abinci, kuma shugabar jam'iyyar PDI - ita ce mace ɗaya tilo a cikin jerin 'yan takarar 10.

Ta taɓa tsayawa takara a ƙarƙashin Déby père a watan Afrilun 2021, inda ta zo ta uku a sakamakon da aka fitar majalisar tsarin mulkin ƙasar ta fitar a hukumance, bayan Pahimi Padacké Albert da ya zo na biyu a wancan lokacin.

Shi ma tsohon firaministan ƙasar, Pahimi Padacké Albert shi ma na daga cikin 'yan takarar da za su baje-hajarsu a zaɓen na watan gobe.

Baya ga waɗannan 'yan takara uku da ake hasashen fafatwar za ta fi zafi tsakaninsu, akwai wasu mutum bakwai da su ma ke cikin 'yan takarar.

Jerin 'yan takarar da za su fafata a zaɓen shugaban ƙasar Chadi

Asalin hoton, Getty Images

.
Bayanan hoto, Tsohon firaministan ƙasar, Pahimi Padacke Albert, na daga cikin 'yan takarar da ke kan gaba a zaɓen
  • Alladoum Djarma Baltazar
  • Assyongar Masra Success
  • Bebzouné Bongoro Theophile
  • Lydie Beassemda
  • Mahamat Idriss Deby Itno
  • Mansiri Lopsékréo
  • Mbaimon Guedmbayë Brice
  • Nasra Djimasngar
  • Pahimi Padacke Albert
  • Yacine Abderamane Sakine

Waɗannan 'yan takara - waɗanda suka fara yaƙin neman zaɓe a farkon makon da muke ciki - za su san makomarsu bayan fitar da sakamakon zaɓen da za a gudanar ranar 6 ga watan Mayu.

Yaya ake fitar da sakamakon zaɓe a Chadi?

Sabuwar dokar zaɓe da majalisar riƙon ƙwaryar ƙasar ta sanya wa hannu, ta yi tanadin cewa ba za a wallafa sakamakon zaɓe a rumfunan zaɓe ba, bayan an ƙidaya ƙuri'u.

Wanda a baya ba haka ake yi ba, sannan kuma ba za a bai wa wakilan jam'iyyu kofin takardun sakamakon da aka samu a rumfunan zaɓen ba.

Wani abu da 'yan hamayya suka bayyana da ci baya, da kuma yin rufa-rufa a sabgar zaɓen.

Hukumar kula da shirya zaɓen ƙasar, ANGE na da kwanaki 15 bayan zaɓen domin ayyana sakamakon zaɓen.

Rassan hukumar ta ANGE za su riƙa tattara alƙaluman sakamakon zaɓukan bayan rufe rumfunan zaɓe, bayan hukumar da ke ƙidaya ƙuri'an ta kammala ƙidayawar, kamar yadda sashe na 67 na dokar zaɓen ƙasar ta tanadar.

Hukumar zaɓen a matakan gunduma za ta riƙa wallafa sakamakon zaɓen, yayin da hukumar ANGE za ta riƙa adana sakamakon rumfar zaɓe bayan rumfa.

Dangane da sakamakon ƙarshe

Asalin hoton, Getty Images

..
Bayanan hoto, A ƙarshen makon da ya gabata ne aka fara yaƙin neman zaɓe a ƙasar.

A Chadi, majalisar tsarin mulkin ƙasar ce ke da alhakin bayyana sakamakon ƙarshe na zaɓen shugaban ƙasar.

Hukumar ANGE za ta aika sakamakon zaɓen zuwa ga babbar kotun ƙasar wadda za ta tantance duka matsalolin da aka samu a lokacin zaɓen.

Wa'adin ƙarshe na bayyana sakamakon zaɓen ya danganta da yadda 'yan takara suka buƙaci hakan, ko suka gabatar da ƙorafinsu.

Idan aka samu gardama, majalisar tsarin mulkin ƙasar na da kwanaki 15 bayan samun sakamako ta bayyana shi ga jama'ar ƙasa.

Idan ba a samu wata matsala ba, kuma majalisar tsarin mulkin ƙasar ta ga cewa an gudanar da zaɓen kamar yadda ya kamata, za ta iya fitar da sakamakon zaɓen cikin kwana 10, bayan hukumar ANGE ta aike mata da sakamakon, kamar yadda sashe na 144 da 145 na dokar zaɓen ƙasar ya yi tanadi.

A wannan zaɓe da aka tsara gudanarwa ranar 6 ga watan Mayu, idan babu ɗan takarar da ya yi nasara, hukumar ANGE za ta shirya zaɓen zagaye na biyu, wanda za a yi ranar 22 ga watan Yunin 2024, inda ake sa ran samun sakamakonsa ranar 7 ga watan Yuli wato mako biyu bayan ranar zaɓen zagaye na biyun.

Sai kuma sakamakon ƙarshe na zaɓen da ake sa ran samu ranar 20 ga watan Yulin 2024.

People are also reading