Home Back

Kwastam ta kama bindigogi 844, harsasai 112,500 da kontena dankare da kwayoyi a Ribas

premiumtimesng.com 2024/8/24
Customs and rifles
Customs and rifles

Hukumar Kwastam reshen jihar Ribas ta kama wani kwantena dankare da bindigogi 844 da harsasai 112,500 a tashar jiragen ruwa na Onne dake jihar.

Shugaban hukumar Bashir Adeniyi, ya sanar da haka ranar Litini a ofishinsu dake Onne.

“Bisa ga bayanan sirri da muka samu ya nuna cewa kwantena dake da lamba MAEU-165396 ta taso daga kasar Turkey ta iso tashar Onne ranar 21 ga Yuni.

“Baya ga makaman sauran kayan dake cikin kwantenan sun hada da kujeru,bututun ruwa kudin su ya kai naira miliyan 4.

“Hukumar ta kama wasu mutane uku da ake zargin suna da hannu a shigo da makaman inda bayan an kammala bincike za a kai su kotu domin yanke musu hukunci.

Bayan haka Adeniyi ya ce jami’an hukumar sun kama wata kwantena dankare da kwayoyin Tramadol, Cosine da sauran su da kudin su ya kai naira biliyan 9.6.

“A cikin kwantenan akwai belin kaya na gwanjo 720 da kudin su ya kai naira miliyan 144.

Ya ce hukumar ta samu wadannan nasarori a dalilin hada hannun da ta yi da sauran jami’an tsaro a jihar.

Idan ba a amanta ba mai ba shugaban kasa Bola Tinubu shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya koka da yadda ake yawan shigowa da bindigogi da muggan kwayoyi kasar nan inda yake cewa hakan na daga cikin matsalolin da ya sa ake fama da rashin tsaro a kasar nan.

Ribadu ya ce gwamnati za ta ci gaba da kokari domin inganta tsaro a kasar nan.

People are also reading