Home Back

Sallah: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Litinin Da Talata A Matsayin Ranakun Hutu

leadership.ng 2024/7/3
Sallah: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Litinin Da Talata A Matsayin Ranakun Hutu

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Litinin 17 da Talata 18 ga watan Yuni a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan babbar Sallah ta bana.

Da yake bayyana hakan a madadin Gwamnatin Tarayya, Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya taya daukacin al’ummar Musulmi na gida da kuma na kasashen waje murnar sallah ta bana.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar Dokta Aishetu Gogo Ndayako.

Tunji-Ojo ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da koyi da halayen zaman lafiya da kyautatawa da sadaukarwa kamar yadda Annabi Ibrahim (A.S) ya yi.

Ministan ya nanata cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dukufa wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya baki daya.

Daga nan sai ya yi kira ga daukacin al’ummar Musulmi da ‘yan Nijeriya baki daya da su bai wa shugaban kasa hadin kai wajen kokarinsa na bunkasa tattalin arzikin kasa.

Yayin da yake yi wa al’ummar Musulmi barka da Sallah, Ministan ya shawarci daukacin ‘yan Njjeriya da su kuduri aniyar ciyar da kasar nan gaba.

People are also reading