Home Back

Tsohon Gwamnan Katsina Ya Watsar da PDP, Ya Rungumi APC Mai Mulki

legit.ng 2024/5/18
  • Tsohon gwamnan jihar Katsina, Barista Shehu Shema ya watsar da kashin jami'yyar PDP mai adawa a jihar
  • Tsohon gwamnan ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a yau Alhamis 2 ga watan Afrilu a karamar hukumar Dutsin-Ma
  • Jiga-jigan jam'iyyar APC da mukarraban gwamnati da dama sun halarci taron sauya shekar na tsohon gwamna, Shema

Abdullah Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Tsohon gwamnan jihar Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema ya koma jam'iyyar APC.

Shema ya sauya sheka a yau Alhamis 2 ga watan bayan ga watsar da jam'iyyar PDP mai adawa a jihar.

Tun a watan Agustan shekarar 2023 ne Shema ya yi wata ganawa da shugaban APC, Abdullahi Ganduje kan komawa jami'yyar.

Tsohon gwamnan ya goyi bayan Atiku Abubakar a zaɓen shugaban kasa amma a matakin jiha ya yi jam'iyyar APC inda Dikko Umar Radda ya sanu nasara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban jam'iyyar APC a jihar da Hon. Hamisu Gambo (Dan-Lawan Katsina) sun halarci taron sauya shekar tsohon gwamnan a karamar hukumar Dutsin-Ma.

Shugaba jam'iyyar APC a gundumar Shema ya bayyana Barista Shema a matsayin jagora nagari.

Karin bayani na tafe ...

Asali: Legit.ng

People are also reading