Home Back

Hanyoyin da ya kamata abi domin magance faɗan Daba a Kano – Kwamitin Tsaro

dalafmkano.com 2024/7/4

Kwamitin nan mai tabbatar da tsaro da yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Wayoyi, da kuma magance ta’ammali da shaye-shaye, wanda gwamnatin jihar Kano ta kafa, ya ce matsawar ana son a kawo karshen rikice-rikicen faɗan Daba a sassan jihar, sai an ƙara yawan jami’an tsaro musamman ma na Anty Daba, tare da amfani da fasahar zamani a guraren da ake fama da matsalar faɗan Dabar.

Mai magana da yawun kwamitin Kyaftin Abdullahi Bakoji Adamu mai ritaya, kuma masanin tsaro, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano.

Masanin tsaron Bakoji Adamu, ya kuma ce, akwai buƙatar a haɗa kai da ƙungiyoyin sa kai, da kuma masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaro, tare da yin amfani da fasahar zamani, domin ganin an kawo ƙarshen faɗan dabar a sassan jihar Kano.

A cewar sa, “Haɗa kai da Dagatai da masu unguwanni, da kuma ƙirƙirar ayyukan yi ga matasa, tare da koyar da su ƙananan sana’o’i, na daga cikin hanyoyin da za’a gujewa faɗawar su a cikin harkar faɗan Daba, “in ji Bakoji”.

Har ila yau, Kyaftin Abdullahi Bakoji mai ritaya, ya kuma ce akwai buƙatar ƙirƙiro shirye-shiryen gyara wajen keɓance riƙaƙƙun ƴan Daba a guraren da ake koya musu sana’o’i, ta yadda za’a kawar musu da sha’awar harkokin faɗan Dabar a tsakanin al’umma.

People are also reading