Home Back

Badakalar Neman Gurbin Aiki: Kotu Ta Tsare Wasu Ma’aikatan Gwamnati Kan Zambar Miliyan 12

leadership.ng 2024/8/23
ICPC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC), ta gurfanar da wata ma’aikaciyar ma’aikatar kasuwanci da zuba jari ta tarayya, Mrs Ndubuisi Joy Cheneme, da Mista Godwin Sabo Takat na ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya bisa zarginsu da karbar kudade ta hanyar yaudarar karya da nufin samo guaraben ayyukan yi ga wasu.

Hukumar ta ICPC a kan tuhumar mai lamba CR/243/2024, wacce ta gurfanar ga Honourable Justice C.O. Oba na babban kotun tarayya mai lamba 31 da ke zaune a Apo, Abuja, ta zargi wadanda ake tuhuma da damfarar masu neman aiki kudade har sama da naira Miliyan 12 (N12,000,000).

ICPC a cikin tuhume-tuhume guda 9, ta zargi wadanda ake tuhumar da karbar wannan kudaden daga hannun wadanda abin ya shafa ta hanyar karya da yaudara.

Lauyoyin wadanda ake tuhuma biyu, Mista E.E. Ogar da I.O. Nweze sun gabatar da buƙatun beli kuma sun roƙi alkali da ya bayar da belinsu akan sharuɗɗan sassauci don ci gaba da shari’a nan gaba kadan bayan kammala bincike.

Daga nan ne mai shari’a Oba ya amince da bayar da belin wadanda ake tuhuma kan kudi Naira miliyan 2 tare da mutum biyu wadanda za su tsaya wa kowannensu, wanda (kowannen wanda zai tsaya) dole ne ya kasance yana da Naira miliyan 20 a asusunsa da filaye biyu a babban birnin tarayya Abuja.

People are also reading