Jerin Makamai da Kwastam Ta Kama Ana Shirin Shigowa da Su Najeriya Cikin Shekaru 7
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Hukumar kwastam ta shahara da kama makamai da ake kokarin shigowa da su Najeriya.
Ko cikin makon nan hukumar ta sanar da kama dimbin makamai da ake ƙoƙarin shigowa da su Najeriya daga Turkiyya.
Legit za ta tattaro muku lokutan da hukumar ta kama makamai da ake kokarin shigowa da su Najeriya a shekarun baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babu mamaki an yi kame-kame da yawa, amma wadannan sun fi jan hankali sosai.
A watan Janairun shekarar 2017, hukumar kwastam ta kama makamai masu tarin yawa a jihar Legas.
Makaman sun hada da bindigogi guda 661 da aka boye cikin manyan akwati guda 49, rahoton Channels Television.
Bincike ya nuna cewa an kera bindigogin ne daga kasar Sin aka biyo da su ta Turkiyya domin shigo da su Najeriya.
A watan Disambar shekarar 2021 hukumar kwastam ta kama makamai masu yawa ana ƙoƙarin shigowa da su Najeriya.
Mutumin da aka kama da kayan ya yi ikirarin cewa talabijin ya dauko amma bayan an yi bincike sai aka gano bindigogi ne, rahoton the Cable.
A watan Yulin shekarar 2023 hukumar kwastam ta kama nau'in makamai har guda 10 a Legas ciki har da bindigogi da dama.
Hukumar ta tabbatar da cewa a cikin makaman a akwai harsashi jigida 442 kuma ta kama mutane biyu.
Kamar shekarun baya, hukumar kwastam ta kama makamai ana ƙoƙarin shigowa da su Najeriya a cikin makon nan a jihar Rivers.
Shugaban hukumar, Bashir Adeniyi ya ce sun kama bindigogi guda 844 da harsashi guda 112,500 a wannan karon.
Sai dai duk da kamun da hukumar ke yi ana hasashen akwai miyagun da suke wucewa ba a gane su ba kuma ba a ji hukumar na bayyana irin hukuncin da ake yankewa waɗanda ake kamawa ba.
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar kwastam ta Najeriya ta yi bayani bayan mako biyu da ta shafe tana samame kan masu safarar man fetur zuwa ketare.
Hukumar ta yi samamen ne kan iyakokin Najeriya ta sassa daban-daban domin gano barnar da ake tafkawa kan safarar mai.
Asali: Legit.ng