Home Back

Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Sauraren Shari’ar Masarautar Kano

leadership.ng 2024/7/1
Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Sauraren Shari’ar Masarautar Kano

Mai shari’a Liman Mohammed na babbar kotun tarayya da ke Kano ya yanke hukunci a yau Alhamis cewa tana da hurumin sauraren ƙarar da Aminu Babba Dan Agundi ya shigar kan batun tsige Sarki Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano na 15 da gwamnatin jihar Kano ta yi.

Wannan hukuncin ya bai wa Sarki Aminu Ado damar kalubalantar halaccin tsige shi a kotu.

Wannan hukuncin ya biyo bayan umarnin da wata babbar kotun jihar Kano ta bayar na sauya tsige Sarki Aminu Ado da wasu sarakuna huɗu da aka tuɓe.

Hukuncin mai shari’a Mohammed ya tabbatar da cewa shari’ar Sarki Aminu za ta iya ci gaba da gudana, wanda ke nuna dambarwar shari’a kan shugabancin masarautar Kano bai ƙare ba.

Tun da farko dai babbar kotun tarayya ta bayar da umarnin wucin gadi na hana gwamnatin jihar Kano aiwatar da dokar masarautar jihar ta 2024, wanda ya kai ga tsige Sarki Aminu Ado.

Duk da tsige shi da kuma naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16 da Gwamna Abba Yusuf ya yi, Sarki Bayero na ci gaba da yin sha’anin mulki a matsayin Sarki, inda ya ci gaba da zama a wata ƙaramar fada da ke Nassarawa a ƙarƙashin umarnin kotu.

People are also reading