Home Back

InnalilLahi: An Shiga Jimami Bayan Rasuwar Jigon APC a Saudiya Yayin Aikin Hajji

legit.ng 2024/7/8
  • An shiga jimami bayan jigon jam'iyyar APC ta riga mu gidan gaskiya a kasar Saudiyya yayin aikin hajji
  • Marigayiyar Ramota Bankole ta kasance jajirtacciya a jam'iyyar APC wacce ta rike mukamai da dama
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jami'yyar a jihar, Seye Oladejo ya fitar a yau Alhamis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Makkah, Saudiyya - Hukumomi sun sanar da rasuwar wata Hajiya kuma jigon jam'iyyar APC a kasar Saudiyya.

Marigayiyar mai suna Ramota Bankole ƴar asalin jihar Lagos ta rasu a kasar yayin da take aikin hajji.

Bankole kafin rasuwarsa, ita ce tsohuwar sakatariyar jin dadi ta jam'iyyar APC a jihar Lagos, cewar Daily Trust.

Sakataren yada labaran jami'yyar, Seye Oladejo shi ya tabbatar da haka a yau Alhamis 20 ga watan Yunin 2024, Vanguard ta tattaro.

"Rasuwarta ya zo mana da bazata da kuma jimami, tabbas ta kasance jajirtacciya a jam'iyyar APC."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Bankole ta kasnace mai hidima ga APC wacce ta ke kokarin fadakar da mata kan shiga siyasa, Allah ya mata rahama."

- Seye Oladejo

Alhaji daga Plateau ya rasu a Saudiyya

A wani labarin, kun ji cewa Wani Alhaji da ya fito daga jihar Plateau, ya riga mu gidan gaskiya a ƙasa mai tsarki wajen gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024.

Sakataren hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar, Alhaji Hayabu Dauda, ya tabbatar da rasuwar Alhajin mai suna Ismaila Musa, a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.

Alhaji Hayabu Dauda ya bayyana cewa Alhajin ya rasu ne a asibitin ƙwararru na Annur da ke birnin Makkah, inda ya shafe makonni uku yana jinya.

Asali: Legit.ng

People are also reading