Home Back

Hukumar Zabe Ta Sanya Ranar Zaben Kananan Hukumomi Ana Cikin Takaddama a Rivers

legit.ng 2 days ago

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Rivers (RSIEC) ta sanya ranar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar.

Hukumar zaɓen ta sanar da ranar 5 ga watan Oktoban 2024 a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a faɗin jihar Rivers.

An sanya ranar zaben kananan hukumomi a Rivers
Za a gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Rivers a watan Oktoba Hoto: Sir Siminalayi Fubara Asali: Facebook

Sanarwar na zuwa ne yayin da ake ci gaba da taƙaddama kan kujerar shugabancin ƙananan hukumomi a jihar, cewar rahoton jaridar The Nation.

Taƙaddamar dai ta faru ne sakamakon rikicin da ke tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da ƴan majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin Martins Amaewhule.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ƙaddamar da shugabannin riƙon ƙwarya na ƙananan hukumomin yayin da tsofaffin ciyamomin suka tubure cewa har yanzu suna kan mulki bayan ƙara musu wa'adin watanni shida da ƴan majalisar ƙarƙashin jagorancin Amaewhule suka yi.

Domin kaucewa ɓarkewar rikici, ƴan sanda sun kulle dukkanin sakatariyoyin ƙananan hukumomin jihar guda 23 har zuwa lokacin da kotun ɗaukaka ƙara za ta yi hukunci kan ƙarar da aka shigar a gabanta.

Asali: Legit.ng

People are also reading