Home Back

Shugaban Turkiyya zai gana da Shugaban Hamas

dw.com 2024/5/14
Shugaban Turkiyya da shugabannin Falasdinawa da kuma Hamas
Hoto: Mustafa Kamaci/Anadolu Agency via REUTERS

Shugaba Racep Tayyip Erdogan na Turkiyya ne ganawa da shugaban kungiyar Hamas ta Falasdinu, Ismail Haniyeh a birnin Santanbul domin tattauna halin rikicin da Zirin Gaza ke ciki.

Sai dai ba a bayyana karin bayani kan yanayin da tattaunawar za ta kasance ciki ba tsakanin bangarorin biyu. A ranar Larabar da ta gabata ce dai, Haniyeh ya gana da ministan harkokin wajen Turkiyya, Hakan Fidan a Qatar kan batun tsagaita bude wuta a Zirin da kuma sakin wadanda aka tsare da su.

A farkon wannan makon ne dai Shugaba Erdogan dai ya soki Firanministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a kan abun da ya bayyana a matsayin kisan kiyashi a Gaza. Sai dai kuma Isra'ila ta nisanta kanta da kalaman shugaban.

Ko da yake duk da zafafan kalaman na Shugaba Erdogan, a baya-bayan nan Turkiyar ta yi kokarinta na shiga tsakani domin sasanta rikicin na Gaza.

People are also reading