Home Back

Atiku Ya Ragargaji Tinubu Kan Dawo da Tallafin Man Fetur a Ɓoye

legit.ng 2024/7/1
  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi magana kan yadda Bola Ahmed Tinubu ke jagorantar Najeriya
  • Atiku Abubakar ya ce akwai lauje cikin naɗi kan yadda Bola Tinubu ya gaza yiwa ƴan kasa bayani kan lamarin tallafin man fetur
  • Ya ce Najeriya ba za ta taɓa cigaba ba idan dai Tinubu zai cigaba da yiwa kasar tuƙin ƴan koyo kuma yana nuna cewa ya ƙware

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki Tinubu kan yadda yake tafiyar da mulkin Najeriya.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa akwai tarin matsaloli da suka dabaibaye tattalin arzikin kasar da Bola Tinubu ya ki bayyanawa.

Atiku da Tinubu
Atiku ya zargi Tinubu da dawo da tallafin mai a boye. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar Asali: Facebook

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku Abubakar ya ce cikin abubuwan da Tinubu ya ki bayyanawa akwai dawo da tallafin mai a sirrance.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku: muna son bayani kan tallafin mai

Atiku Abubakar ya bayyana cewa tun kwanaki ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya fito ya bayyanawa yan Najeriya yadda ake ciki bayan ya cire tallafin man fetur.

Ya ce akwai bukatar yan Najeriya su san ina kudaden tallafin suka shiga kuma wane cigaba aka samu bayan cire tallafin amma abin ya gagara.

Kudin tallafin man fetur ya karu

Atiku Abubakar ya ce ana cikin bukatar sanin kudin da gwamnati ta tara bayan cire tallafi sai aka ji kudin tallafin da gwamnati ke kashewa ya karu.

Tsohon shugaban kasar ya ce a shekarar 2023 an kashe Naira tiriliyan 3.6 amma bayan Tinubu ya cire tallafi kuma an kashe Naira tiriliyan 5.4 a 2024.

Najeriya na tafiya ta baya-baya

Saboda haka Atiku ya ce Najeriya ba ta tafiya a seti ƙarƙashin Tinubu kuma akwai bukatar ya yiwa ƴan ƙasa gamsasshen bayani.

Atiku ya ce Bola Tinubu ya dawo da tallafi a boye amma kuma kullum yana cewa ya cire tallafi saboda tukin ƴan koyo yake.

Atiku ya gana da Peter Obi

A wani rahoton, kun ji cewa manyan ƴan takarar shugaban ƙasa a 2023, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP sun gana yayin da ake shirin zaɓen 2027.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku ya ce abin alfahari da girma ne da ya karɓi bakuncin tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi.

Asali: Legit.ng

People are also reading