Home Back

Rashin Bayar Da Wadataccen Kudin Cefane Ga Mata

leadership.ng 2024/6/29
aure

Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da korafe-korafen da mata ke yi kan mazajensu, musamman wajen karbar kudin cefane. Da yawan mata na korafin wannan matsala ga mazan da suke da wadata sosai amma ba sa iya bayar da kudin cefane yadda ya kamata sai dai su bayar da shi kat da kat ba tare da canjin da za a samu har a toshe wata mafakar ba, kamar misali; za su iya yin bakin da za su ba su kudin mota, ko wata larura ta faru ga yara ko su kansu matan da za su iya bayarwa a siyo magani, ko kuma wata tafiya ta ujila ta zo musu wadda dole su kashe kudin mota.

Mata na kara korafin cewa; koda ace suna da wata sana’ar watarana sukan rasa kudi a hannu. Matan na korafi ne a kan yadda maza masu wadata suke kasa bayar da wadataccen kudin cefanen daya kamata, sai dai su ce suna bukatar girki na musamman ba irin wanda aka saba na yau da kullum ba, wanda kudin da suke bayarwa baya isa girkin da suke bukata.

Dalilin hakan ya sa shafin Taskira jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; Ko me za a ce akan hakan? Shin hakan daidai ne ko kuwa?, Me yake janyo hakan, kuma wane matsaloli hakan ke iya haifarwa?, Ta wacce hanya za a iya magance wannan matsalar?
Ga dai bayanan nasu kamar haka:

Sunana Fatima Bala Sani (Aunty), Daga Jihar Kano:

Mata

Yau dai Taskira ta tabo min abun da ke ci min tuwo a kwarya, batun kudin cefane, wanda duba da yanayin da ake ciki ya kamata maza da mu matan mu yi wa junan mu adalci, matsayinka na maigida kuma mai shi bai kamata ka tsuke aljihunka ba wurin bada kudin cefane ba. Mu ma kuma mu kasance masu tattali da sanin dabarun girki ta yadda ko yaya muka yi shi zai ciwu, idan muka yi duba da da-can baya da babu kayan dandano kuma abincin na ciyuwa me ya sa mu yanzu ga komai da komai amma wasu in suka yi abincin ba zai ciwu ba? Rashin iyawa ne? Ko kuwa sakacin mu ne? Wannan dalilin ne ya sa mazajen basa bamu isashshen kudin cefanen ko kuwa? Batun gaskiya hakan ba dai dai ne ba in fact bai ma kamata ba ace ka ajiye mace a gida babu isashshen kudi kuma alhalin kana da wadatar, koda kuwa kana wadata ta da komai na cefane ya dace ace ka ware wasu ‘yan canji da za ka rika bata duk sati, sati biyu ko duk karshen wata, hakan zai taimaka mata wajen rage tare da magance wasu kananun matsolinta ba tare da tayi maka magana ko ta dameka da bani-bani ba. Ba komai ke janyo hakan ba ga wasu mazan ji su idan suka dauki kudi suka bawa mace ji suke kamar duniya suka mallaka mata, bayan mu mata duk abun da muke samu karshensa dai wa mazan yake komawa. Babban matsalar da hakan za ta janyo shi ne damuwa ga ita macen da rashin yarda a tsakaninta da danginta ko ‘yan’uwanta, ana ganin tafi karfin yi ko bada wata gudunmawa daga gareta amma sai ya gagareta saboda mijinta bai wadata ta ba. Hanyoyin da za a bi dan magance wannan matsalar shi ne; idan ba zai rika bata isashshen kudi a hannunta ba, ya rika siyayyar cefanen komai da komai na masarufi sannan su ware wasu kudade da za su rika basu duk karshen wata, ke ma a matsayinki na mace ki kasance mai tattali da saka albarka a duk abun da aka samu, mu mata muna cire albarkar abu ba tare da mun sani ba ta rainuwa tun kan kiyi amfani da shi hakan na cire albarkar shi duk yawan shi kuwa, komai kankantar shi cene Allah ya sa albarka da kyakyawar niyya za ki ga canji a al’amuranki na yau da kullum.

Sunana Rabiatu Bashir (Ummu Maher Mrs Green), Daga Tarauni, Jihar Kano:

Mata

Gaskiya a fahimta ta bai kamata namiji ya bawa matarsa kudin da ba zai ishe ta ba, amma idan har da halin yin hakan, wasu kuma mugunta ce take damunsu, amma muguntar kai ce domin idan ka bayar da wanda zai isar kai ma za ai maka me dadi. Gaskiya ba daidai bane, domin yin hakan zai sa ka koya wa matarka sata. Abin da yake janyo hakan abu biyu ne mafi yawanci, talauci, rowa, idan mutum talaka ne sosai babu yadda zai yi, wani kuma marowaci ne ko yanada shi sai ya hana. Zai iya jefa mace a wani hali, daga nan ta fara yi maka sata ko yawace-yawace da yawan roko. Hanyar da za a magance sunada yawa, ko dai mace ta nemi na kanta ko kuma mijin ya canja halinsa, domin nan gaba matsalar za ta zama babba ka koyawa matarka sata. Shawarar da zan bawa maza masu wannan halin shi ne; su ji tsoron Allah, sannan su san kiwo Allah ya basu kuma zai tambaye su,
matan da suka tsinci halinsu a cikin wannan hali mafita daya su nemi sana’a, yadda koda ba a basu ba za su cika.

Sunana Fatima Tanimu Ingawa, Daga Jihar Katsina:

Wannan gaskiya ne, an ce “Miya mai dadi kudi ne yai aiki” In har ana so a ci mai kyau abinci mai sunan abinci to fa dole a kashe masa ‘yan kwabbai musamman a wannan lokaci na tsadar rayuwa. Gaskiya ya kamata maza su gane su gyara, su san cewa fa rayuwar kullum canzawa take komai na kara daraja, ya kamata suna sabunta kudin cefannan nan ma’ana a rika kari duba da yanayin rayuwa, a wannan rayuwa hakuri ake ba sai an rufa an tada kai ba. In ma aka samu mai kyaun da za a tarbi baki da shi ya wadatar sai a hassafa da abun da kenan in akwai halin hakan. Mata ba sai an sa dogon buri a kan kudin cefane ba ta yadda karshe ba za a samu ingantacciyar cima ba amma an kule ana zubin dashi. Rayuwar yau tana tattare ne da kalubale da kuma uzuri, bahaushe na cewa shimfidar fuska ta fi ta tabarma. Ni a ganina a bawa bakin tarba da abinci mai kyau ya ma fi kudin. In ya sa in da halin bada kyauta a yi. Don bahaushe na cewa; “Da babbar rowa gara karamar kyauta”. Hanyar da za a magance hakan shi ne; tsari wato (plan) saboda rayuwar yanzu ba a yinta da ka sai ana tsara yadda abubuwa za su kasance cikin yardar Allah, gwargwado a ware ma cefane hakkinsa ta yadda yara masu tasowa za su samu cima mai kyau kar wai mace ta matsa lallai sai ta rika tatsar wani abu a kudin cefanen nan. Ai kokarin kwatanta ma mazajen, inda hali a lissafa masu yadda abubuwa suka canza ta yadda za su rika badawa da gwasama. A samu dai a ci mai kyau a sha mai kyau don ingantattuwar lafiya, Allah-bar-shi dan kwabo-darin da ke shigo maki ta wata hanyar wala’Allah sana’a ce ko kuma mijin na da rufin asirin da ya ke dan yaga maki, sai ki rika hassafawa da wannan da kuma rage wasu ‘yan bukatocin da ka taso, Allah ya mana jagoranci amin.

Sunana Usman Fawziyya Daga Jihar Adamawa:

Mata

Ni a ganina mace bai ma kamata ta rinka karbar kudin cefene ba a irin wannan marra da muke ciki din nan kawai rubuta mishi abin da ku ke bukata a gidan ya je kasuwa da kanshi yayi cefenen gidan, shi daman addini ma bai ce mace ce za ta shiga kasuwa cefene ba hakkin shi ne yayi miki in kuma ya zamana ba mazauni bane to, dole ne a matsayin ki na matar gida ku zauna da shi kiyi mishi dalla-dalla yadda zai gane abin da yake bayarwa baya isar ku cefene ya kamata ya kara wani abu, in kuma ya ce ba zai kara ba to, fa dole ku sake zaman shawara ke da shi ki san yadda za ki yi dai kar ya barki da ciyar masa da gida da shi kanshi. Shawara ga maza don Allah ku gyara kun san yadda komai yayi tsada ba abin da bai yi tsada ba a kasuwa a taimaka a sassauta ma mata ka dauko ta daga gidan iyayenta ta dawo karkashinka dole ne ka ciyar da ita yadda ya kamata ba wai kuma ka bar ta da ciyar maka da gida ba, sai shawara ta ga mata Allah ya kara mana hakuri a gidajenmu amma kar ki bari ya cutar dake don ke ma kina da hakki a kanshi, Allah ya sa mu dace.

Sunana Ayshatu D. Sulaiman Daga Jihar Gombe:
Gaskiya ya kamata maza su sani muddun kana da shi ka ki bata wanda zai isheta dan ka kuntata mata Allah shi ma zai kuntata maka, tunda annabin mu bai koyar da hakan ba, sannan kun ce kuna koyi da shi, idan kuma babu ne to, ya ke ‘yar’uwa ki yi hakuri da dukkan abin da ya kawo miki komai mai wucewa ne. Tabbas kina baki kina dan siyan wani abu to, ya kamata ki koyi kowacce sana’a wacce za ta rika kawo miki biyar goma idan ki ka yi hakan kin huta. Duk da cewa idan kina sana’a wataran akwai yai da gobe, shi ya kamata idan ya ga kin gazaya kamata ya tallafa miki. Abin da yake janyo hakan ni a ganina akwai son kai, da kuma rashin tausayi, amma idan namiji ba shi da shi to, sai ki yi hakuri. Shawarar da zan bawa maza shi ne; Su ji tsoron Allah muddin ba wai babu bane, su sani in su ne suka je kasuwar ba za su iya sarrafa wannan kudin da suka baki ba sai sun kara a kai sosai, dan haka ya kamata su gane su rika yin komai daidai gwargwado. Shawara ga mata idan mijinki ba shi da shi ya baki kadan ki yi hakuri ki sarrafa, in kuma akwai ya hanaki ki ce ya cefano ya kawo miki komai da komai, idan kuma kina sana’a kina samun kudi ki yi hakuri wataran zai kara miki.

Sunana Hussaina malami (Haseenan Masoya), Daga Gwarzo, Jihar Kano:

Mata

Irin kalubalen da mata suke fuskanta a gidajensu tabbas akwai maza masu tausayin Iyalinsu akwai kuma azzaluman maza shi ya sa idan Allah ya hada ki da miji nagari ki godewa Allah, mafi akasari maza a yanzu koma na ce har da basa iya ba mata cikakken kudin cefane sai ku ga miji zai futo ya mikowa mace naira 500 da zummar kudin cefane, kuma fa macen tana da ‘ya’ya ya bata 500 a ciki za ta siyo man girki farin mai ke nan a ciki za ta siyi kayan miya a ciki za ta sayi magunan girki wata ma har da iccen da za ta yi amfani da shi to, dan Allah ta ya wannan kudi zai isheta sannan shi mijin zai futa waje ya je ya cika cikinsa da abinci me dadi wata kilama ‘Restaurant’ za shi ya ci me kyau ya sha me kyau sannan ya dawo gida idan ya dawo gidan ko kallon abincin nasu ba zai yi ba saboda ya san bai bada mai dadi ba. Sannan wani ga kudin a jikinsa amma ya gwammace ya fita ya je ya kashe ma “yan mata ga rashin sutura wadatacciya duk da yanzu akwai yanayi na rayuwa, amma wasu nada shi tsabar rashin adalci ne, ire-iren abubuwa makamanta dai suna faruwa Allah ya sa mu dace su kuma mazan Allah ya sa su gane.

Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:

Mata

To magana ta gaskiya dukkanin Maigida yana so a gidansa aji dadi don haka muddun yanada wadata to kuwa zai yalwata sosai ba wai a wajen cefane kadai ba harda sauran bangarorin walwalar iyali, amma idan babu hali dole ne ayi hakuri da abun da ya samu, domin dama so baya zama samu a kowane lokaci. To indai akwai halin badawa da yawa kuma Maigida yayi kwauro to sam-sam bai dace ba, domin yanada kyau mutum yake kyautawa iyalansa muddun akwai halin hakan domin hakan zai taimaka wajen kara samun budi a wajen nema kuma zai sa iyalansa a cikin walwala da farin ciki. To ni dai a nawa tunanin talauci ko babu shi ne yake jawo haka, domin indai Maigida yanada halin samar da walwala a cikin iyalansa to zai yi kokarin haka domin sune abu mafi kusanci da kauna a gare shi, don haka dole zai yi kokari wajen ganin ya kyautata musu bakin gwargwadon halin sa, maganar kuma matsaloli to ni a ganina babu wata matsala sai dai idan dama abun duniya take so ba wai mijin ba ko zaman auren. To hanya ta farko dai ita ce a dage da neman halak da kuma addu’ar Allah ya ba mu arziki ta hanyar halak domin dukkanin Maigida ya yalwatawa iyalansa dama ‘yan’uwa, su kuma iyayen mu mata suke hakuri da abun da ya samu kuma a dage wajen yi wa mazaje addu’ar Allah ya buda musu sai ka ga Allah ya kawo mafita gaba a wannan matsala.

Sunana Hassana Sulaiman, Hadejia A Jihar Jigawa:
Alhamdulillah kusan da farko abin da ya kamata mu fara tofawa kan wannan maudu’in na yau dan hakika kusan mata da dama idan za a iya zama da su wannan halin kusan kaso 70% cikin 100% suna fuskantar wannan matsalar cikin gidajensu na aure, kuma abin da suka saka a gabansu shi ne hakuri da yanayin nan da suka tsinci kansu suke yi, dan babu wata hanya da ya kamata su yi ko su bita da ya wuce yin hakurin nan. Gaskiya indai gaskiyar za a fada hakan ba daidai bane amman fa matukar suna da halin bada mai yawan da zai isan ayi duk wani abun da ya dace ayi din a nawa mahangar, to amman kuma idan babu ce ta saka hakan za mu iya cewa sun yi daidai da bada dan abin da ya hore musu sai a karba ayi hakuri ita matar. Kusan abin da ke janyo hakan musamman ga mazajen da suke hakan wasu ma iya cewa rashin sanin hakkokin auren na tun farko shi ya sa yake iya ma yin hakan, wasu kuma kawai dai irin suna da dan mako din nan ne na rashin bada abin da zai isa a cikin gidan nasu, wasu kuma kawai suna kyashin bawa matan ne kudin da zai iya isar su yin abinci sai sun zo suna hada can kama can sannan za su iya samarwa da abincin yayi yadda ake so, sannan kuma wasu mazan a cikin gidan ne ba za su bada mai yawan ba ne amman kuma za su fita waje su kashewa cikinsu fiye da abin da idan suka bada a gidan za a iya samar musu da shi. To kusan hanyar da za a iya magance wannan matsalar bai wuci namijin ya ji tsoron Allah ba, ya kuma san daga cikin hakkokin da ubangiji ya dora masa akwai masu tarin yawa wanda matar tana ciki ‘ya’yansa suna ciki, sannan kuma ya sani cewa duk wani abu da ya aiwatar dan musgunawa iyalansa ubangiji na kama shi da wannan laifin matukar yanada sani akai, idan kuma bai da sani ya kamata yana tuntubar malamai dan kada ya fada cikin halaka.

Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Daga Rano, Jihar Kano

Mata

Abin da zan iya cewa shi ne ku mata ku sani bawai don ina namiji bane a’a kowa ya san halin da ake ciki a yanzu kada ku ce za ku sami wadannan abubuwan da ku ka zayyano ayi hakuri da abin da aka samu iyakaci idan an riski daya daga cikin wadancan larurorin da bukatun bazata to sai a kira maigida a gaya masa ga abin da ya faru bayan fitarsa don haka koda girkin ne ba a yi wanda yake bukata ba na san zai yi uzuri in sha Allah a dinga rage buri domin wallahi yanzu ba kowane yake fita nema yake samu ba. Wasu idan suna da halin kyautatawa suka ki ba daidai bane amma wadanda samunsu ba karuwa yayi ba kuma da ma can ba mai yawa bane sai asuba tashin kayayyaki na yau da kullum ayi musu uzuri ayi amfani da iya abin da suka bayar. Kuncin matsin rayuwa yanzu shi ne ya sa wasu hakan sannan wadanda suke da halin kuma suka ki kyautatawa don sun sami matsala su zargi kansu. Amma kuma fa su ma matan suna duba yanayi domin kullum mai makon ace abu kasa ya ragu sai dai ka ji an ce ya karya kinga kuwa su ma magidanta dole suna dan yin tanadin gaba.

People are also reading