Home Back

Ba don Azumi da na yi na kwanaki 21, da an yi tashin duniya ranar 25 ga Afrilu kamar yadda aka yi min wahayi – Fasto Metuh

premiumtimesng.com 2024/5/15
Ba don Azumi da na yi na kwanaki 21, da an yi tashin duniya ranar 25 ga Afrilu kamar yadda aka yi min wahayi – Fasto Metuh

Faston da ya ce Allah ya yi masa wahayin cewa za ayi tashin duniya ranar 25 ga Afrilu, ya bayyana dalilin da ya sa Allah ya dakatar da tashin duniya da ya ce an yi masa wahayin za a yi.

Idan ba a manta ba, Fasto Metuh ya wallaha a shafin sa a yanar gizo cewa Allah ya yi masa wahayin za a yi tashin duniya ranar 25 ga Afrilu.

Sai dai kuma ranar ta zo ta wuce shiru ba a ga wani abu mai kama da tashin duniya.

Daga baya sai wannan Fasto ya ce mutanen duniya su gode masa, badun Azumi da ya rika yi ba tare da wasu waliyai da ke tare da shi a cocin sa da tuni duka an sheka lahira ana can ana fama da hisabi.

” Da ni da wasu waliyai bayin Allah muka dukufa azumin kwana 21 muna rokon Allah ya yi wa mutanen duniya hakuri kada a naɗe duniyan.

People are also reading