Home Back

Bayern Munich na son Silva, Arsenal da Chelsea na son Nico Williams

bbc.com 2024/10/6

Asalin hoton, Getty Images

.
Bayanan hoto, Bernardo Silva

Bayern Munich na son dan wasan Portugal Bernardo Silva mai shekara 29, kan farashin fam miliyan 50 duk da har yanzu sauran shekara biyu kwantiraginsa da Manchester City ta kare. (Star)

Borussia Dortmund na gab da kammala yarjejeniya kan dan wasan tsakiya na Jamus mai taka leda a Brighton Pascal Gross, mai shekara 33 wanda kwantiraginsa zata kare nan da shekara guda. (Sky Sport Germany)

Shugaban Arsenal Mikel Arteta ka shiga tsaka mai wuya wajen batawa wasu daga cikin manyan 'yan wasansa rai, idan ya dauko dan wasan Sifaniya mai taka leda a Athletic Bilbao, Nico Williams, mai shekara 21kamar yadda dan wasan ya bukata. (Express)

Chelsea ma na son Williams, ko da ya ke ya na daga cikin wadanda kungiyar Paris St-Germain ke son dauka, idan dan wasan gaba na Faransa Kylian Mbappe, ya bar kungiyar zuwa Real Madrid. (Teamtalk)

An tuntubi tsohon mai kai hari na Manchester United , Ruud van Nistelrooy a wani bangare na horas da 'yan wasa da sabon koci Erik ten Hag ke yi. (Fabrizio Romano),

Newcastle United na shirin sayar da Callum Wilson, 32, idan har sun cimma yarjejeniya da dan wasan Ingila Dominic Calvert-Lewin, 27, mai taka leda a Everton. (Football Insider)

Manchester United da Liverpool na son dan wasan Lille, kuma mai tsaron gida na Faransa, Leny Yoro sai dai dan wasan Faransar mai shekara 18, na son komawa Real Madrid. (Marca - in Spanish)

Liverpool, da Manchester City da Arsenal na cikin kungiyoyi biyar da ke ci gaba da zawarcin dan wasan tsakiya na Jamus Joshua Kimmich mai shekara 29, idan dan wasan ya bar kungiyar Bayern Munich. (Sky Sport Germany)

People are also reading