Home Back

Idan na fadi abinda ya faru tsanina da Kloop za a samu matsala - Salah

bbc.com 2024/5/9
Salah Kloop

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan Liverpool, Mohamed Salah ya ce zai tayar da zaune tsaye idan ya fadi abinda ya faru tsakaninsa da Jurgen Kloop ranar Asabar.

Liverpool ta tashi 2-2 a gidan West Ham United a wasan mako na 35 a Premier League da suka fafata.

Salah da Kloop sun mayar wa da juna kalamai a lokacin da dan kasar Jamus zai saka dan kwallon tawagar Masar cikin fili a minti na 79, domin canji dan wasa.

Kloop ya ce ba zai taba fadin abinda suka cewa jina ba, amma tsohon dan kwallon Liverpool, Peter Crouch ya sanar da TNT Sports cewar ''lamarin ba zai yi wa kungiyar dadi ba.''

Crouch ya ce'' Salah dan kwallo ne da ake fara wasa da shi a Liverpool a yawancin wasanni, kenan ba zai ji dadi a ajiye shi a benci, bayan lafiyar kalau.''

''Amma ba wanda ke fatan hakan na faruwa tsakanin kociya da fitatcen dan wasan kungiya.''

An nuna ran Salah ya baci kamar Kloop ya fada masa wata magana da bai gamsu ba a lokacin da zai yi canji, inda shima yake mayar da martani har da ta kai Darwin Nunez da Joe Gomez sun shiga tsakani.

Sakamakon tashi 2-2 a gidan West Ham da Liverpool ta yi ranar Asabar, an fitar da kungiyar Anfield daga cikin masu fatan lashe Premier League na bana.

People are also reading