Home Back

Hajji: Abba Kabir Ya Sake Gwangwaje Mahajjatan Kano 3,121 da Goron Sallah

legit.ng 2024/7/3
  • Gwamnan jihart Kano, Abba Kabir ya sake ba mahajjatan jihar goron sallah yayin da suke kasar Saudiyya
  • Gwamnan ya ba mahajjatan 3,121 kyautar riyal 100 domin gudanar da shagulgulan bukuwan sallah
  • Mataimakin gwamnan jihar, Abdulsalam Gwarzo shi ya sanar da haka yayin ziyara sansanin 'yan jihar da ke kasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake abin alheri ga maniyyatan jihar da ke kasar Saudiyya.

Abba Kabir ya gwangwaje mahajjatan da riyal 100 ga mahajjata 3,121 da suka fito daga fadin jihar baki daya.

Abba Kabir ya ba mahajjatan Kano kyautar makudan kudi
Abba Kabir ya ba mahajjatan Kano 3,121 goron sallah a Saudiyya. Hoto: Abba Kabir Yusuf. Asali: Facebook

Kano: Abba Kabir ya gwangwaje mahajjata

Mataimakin gwamman, Abdulsalam Aminu Gwarzo shi ya tabbatar da haka yayin ziyara sansanin mahajjatan da ke Mina a Saudiyya, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwarzo ya ce gwamnan a baya ya cikatawa mahajjatan N50,000 bayan kara kudin aikin hajji da kuma karin N150,000.

Mataimakin gwamnan ya bukaci mahajjatan da su dage da addu'a musamman domin samun zaman lafiya a kasar.

Ya kuma bukace su da su kasance jakadu nagari a Saudiyya wurin kare martabar jihar da kuma Najeriya baki daya.

Daga bisani, Gwarzo ya kai ziyara duka sansanonin mahajjatan na kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar a kasar Saudiyya.

Abba Kabir ya tallafawa maniyyata a Kano

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir ya gwangwaje maniyyatan jihar Kano da kyautar N500,000.

Wannan kyauta na daga cikin tallafi da gwamnan ya bayar bayan karin kudin kujerar hajji a fadin Najeriya a bana.

Asali: Legit.ng

People are also reading