Hajji: Abba Kabir Ya Sake Gwangwaje Mahajjatan Kano 3,121 da Goron Sallah
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake abin alheri ga maniyyatan jihar da ke kasar Saudiyya.
Abba Kabir ya gwangwaje mahajjatan da riyal 100 ga mahajjata 3,121 da suka fito daga fadin jihar baki daya.
Mataimakin gwamman, Abdulsalam Aminu Gwarzo shi ya tabbatar da haka yayin ziyara sansanin mahajjatan da ke Mina a Saudiyya, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwarzo ya ce gwamnan a baya ya cikatawa mahajjatan N50,000 bayan kara kudin aikin hajji da kuma karin N150,000.
Mataimakin gwamnan ya bukaci mahajjatan da su dage da addu'a musamman domin samun zaman lafiya a kasar.
Ya kuma bukace su da su kasance jakadu nagari a Saudiyya wurin kare martabar jihar da kuma Najeriya baki daya.
Daga bisani, Gwarzo ya kai ziyara duka sansanonin mahajjatan na kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar a kasar Saudiyya.
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir ya gwangwaje maniyyatan jihar Kano da kyautar N500,000.
Wannan kyauta na daga cikin tallafi da gwamnan ya bayar bayan karin kudin kujerar hajji a fadin Najeriya a bana.
Asali: Legit.ng