Home Back

Kwastam ta kama harsasan da kudinsu ya kai Naira miliyan 557 da aka ɓoye a cikin buhunan Garin kwaki

premiumtimesng.com 2024/4/29
Kwastam ta kama harsasan da kudinsu ya kai Naira miliyan 557 da aka ɓoye a cikin buhunan Garin kwaki

Hukumar hana fasa kwauri ta kasa (NCS) reshen jihar Ogun ta ce ta kama harsasai 940 da kudinsu ya kai Naira miliyan 557 da aka boye a cikin buhunan garin kwaki Idiroko.

Shugaban yankin, Ahmadu Shuaibu ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Juma’a a Idiroko, Ogun.

Shuaibu ya ce yayin da suke gudanar da aikin yaki da fasa kwauri a ranar 14 ga watan Maris, jami’an rundunar sun kama wasu harsasai 940 da aka boye a cikin buhunan Garin kwaki.

Ya bayyana cewa, rundunar ta shafe sama da makonni biyu tana bin sahun su tun daga jamhuriyar Benin.

Sai dai kuma ba a iya kama waɗanda ke ɗauke da waɗannan kaya ba saboda sun arce ne suka bar buhunan garin.

Bayan haka hukumar ta ce ta kama buhu 123 da kulli 3,172 na ganyen Wiwi, fatun jakuna 380; Belin kayan gwanjo 304 da kwalaye 910 na Kaji.

 
People are also reading