Home Back

Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga 3 A Kaduna

leadership.ng 2024/5/18
Sojoji Sun Kwato Makamai Da Babura, Sun Ceto Mutane 3 A Kaduna 

Dakarun sojin Nijeriya sun hallaka wasu ‘yan bindiga guda uku a wani samame da suka kai a Jihar Kaduna.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce ta samu nasarar kashe ‘yan bindigar ne bayan samun bayanan sirri kan wajen da suke zama.

Rundunar ta ce ta yi musu kwanton bauna, inda ta kashe uku daga cikinsu.

Dakarun sojin sun ce sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar kafin kashe uku daga cikinsu yayin samame da suka kai kauyen Kidandan da ke karamar hukumar Giwa a ranar Juma’a.

“Yan bindigar na kan hanyarsu ta zuwa gyara baburansu, wadanda suke amfani da su wajen aikata ta’addanci a Jihar Kaduna kafin su hadu da ajalinsu,” in ji sanarwar.

Sun kuma kwato makamai da suka hada da bindigar Ak-47, harsasai, babura hudu da kuma wani akwatin rediyo guda ɗaya.

People are also reading