Home Back

Rikicin Sarautar Kano: Kwankwaso Ya Caccaki Gwamnatin Tarayya, APC Ta Mayar Da Martani

leadership.ng 2024/7/6
Ganawar Tinubu Da Kwankwaso Alkairi Ce – Mataimakin Shugaban FUDMA

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya zargi gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC kan amsar munanan shawarwari daga makiyan Jihar Kano.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a yayin bikin kaddamar da aikin gina titunan mai tsawon kilomita 82 a mahaifarsa ta Madobi da gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi.

Zargin ya biyo bayan rikicin masarautar Kano, inda rahotanni suna nuna cewa hukumomin tsaro na tarayya na goyon bayan hambararren Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Tsohon gwamnan Jihar Kano, ya jaddada cewa al’ummar Jihar Kano ba za su lamunci duk wani yunkurin yin katsalandan a cikin harkokin da suka jibanci jihar.

“Muna da yawan mabiya domin mutane sun yarda da mu. Sannan kuma mu masu goyon bayan jama’a ne, kuma gwamnatin NNPP ta kudiri aniyar yi musu hidima tun da suka zabe ta,” in ji Kwankwaso.

Ya kuma jaddada kudirin ‘yan Jihar Kano na mara wa gwamnan jihar baya domin cimma burin da ta sa a gaba duk da cewa ana yi mata katsalandan.

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP ya ci gaba da bayyana cewa makiya jihar marasu hankali ke bai wa gwamnatin tarayya shawarar daukar tsauraran matakai kan Jihar Kano ciki har da a kafa mata dokar ta-baci, inda ya sha alwashin cewa al’ummar Jihar Kano masu son zaman lafiya ne kuma ba za su bijire masa.

Kwankwaso ya kuma yi tsokaci kan yanayin siyasar da ke tunkara a zaben 2027, inda ya zargi wasu ‘yan siyasa na shirin tayar da tarzoma.

Ya sha alwashin cewa jam’iyyar NNPP ba za ta bari wadannan abubuwa su murkushe su ba, yana mai cewa, “Muna mai tabbatar wa duk wanda yake tunanin zai iya cin zarafinmu a siyasance, muna tabbatar da cewa a shirye muke mu yake shi.”

Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa ya gargadi gwamnatin tarayya da ta daina sauraron ‘yan siyasa marasa kishin kasa daga Kano, yana mai gargadin cewa irin wannan abu zai haifar da babban baraka.

“Kofarmu a bude take wajen tattaunawa, sulhu, da sasantawa, amma ba za mu amince da tsoratarwa da cin zarafin siyasa ba. Mun san yadda ake yin siyasa kuma za mu yi duk abin da ya dace domin kare kanmu daga duk wani sharri,” in ji Kwankwaso.

A hannu guda kuma, jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta yi kira a kama Kwankwaso.

A cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas ya fitar, ta ce jam’iyyar tana zargin Kwankwaso da haddasa tashin hankali kan zarge-zargen da yake yi wa gwamnatin tarayya.

Abbas ya bayyana cewa babu wata barazana da Kwankwaso zai yi wa gwamnatin tarayya.

“Jagoran jam’iyyar NNPP da ke fama da rikici wanda yake boye rashin aikin da gwamnatinsu ta kasa yi a cikin shekara daya da ta wuce, sannan kuma yana kokarin ganin ya mallaki siyasar Kano, ya kamata jami’an tsaro su kama shi domin ya bayyana wadanda ke daukar nauyin ‘yan ta’addan Boko Haram.

“Muna so mu yi kira ga jami’an tsaro da kakkausar murya da su kamo wannan mutumi domin ya bayyana sunayen wadanda ya kira makiyan Jihar Kano da ke yi wa gwamnatin tarayya aiki domin daukar nauyin ‘yan ta’addan Boko Haram da masu tayar da kayar baya,” in ji sanarwar.

Shugaban jam’iyyar ya yi nuni da cewa wadannan kalamai alama ce ta wata muguwar manufa da Kwankwaso da makarrabansa suka yi na kawo tashin hankali a Kano.

“Kwankwaso ya dade yana zama barazana ga Kano da kasa baki daya bisa la’akari da abubuwan da suka faru a baya. Yana gudanar da wata kungiyar asiri, inda ake zarginsa da daukar matasa aiki wanda akasarin su wadanda suka bar zuwa makaranta domin su tada zaune-tsaye a jihar.”

Abbas ya ce kafin zaben 2023 har ma lokacin zaben, an dauki dubbunnan matasa aiki domin tsoratar da jama’a ta hanyar kai musu hari da lalata dukiyoyin da ake ganin ‘yan adawa ne da kuma sace wayoyin mutane.

Shugaban jam’iyyar ya yi zargin cewa a lokacin da ake tafka shari’a kan zaben gwamna, Kwankwaso da mukarrabansa sun yi wa alkalai barazana.

Abbas ya ce tun bayan da aka maido da Alhaji Muhammadu Sanusi a matsayin sarki, an dauki daruruwan matasa aiki dauke da makamai tare da jibge su a fadar sarkin, lamarin da ke zama babbar barazana ga mazauna cikin fadar da kewaye.

People are also reading