Home Back

‘Ba na fatan sake rayuwa a Fadar Shugaban Ƙasa karo na biyu’ – Patience Jonathan

premiumtimesng.com 3 days ago
Bi-ta-da-kulli Buhari ke min, ba bincike ba  -Patience Jonathan
patience-and-jonathan

Uwargidan tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, Patience Jonathan, ta bayyana cewa ba ta addu’ar Allah ya sake na ya damar sake yin rayuwa a Fadar Shugaban Ƙasa a karo na biyu.

Patience wadda maigidan ta Goodluck Jonathan ya yi shugabancin Najeriya daga 2010 zuwa 2015, tsawon shekaru shida, ta bayyana haka a wani taron Cibiyar Kwararru kan Hulɗa Jama’a.

Ta ce riƙon Najeriya abu ne sai tara wa mutum gajiya sosai. “Ai duk wanda ya kalle Ni yanzu zai tabbatar da cewa na samu hutu sosai. Amma Fadar Shugaban Ƙasa rayuwa ce ta tara gajiya a koda yaushe.

“Duk wanda ya shiga wannan fada ya fito lafiya, to ya ƙara gode wa Ubangiji, domin ya yi ta-barka.

“Ni a yanzu ba na addu’ar sake yin rayuwar a Fadar Shugaban Ƙasa, ko da an sake yi min tayi, ba zan karɓa ba.

“Ni da maigida na ba mu nemi mulki bakin-rai-bakin-fama ba. Ni da shi muna cikin ɗaki zaune, aka kira shi aka ce masa ya faɗi zaɓe. Ban ba shi shawarar ya ƙi amincewa ba. Shi ma da kan sa ya karɓi ƙaddara, saboda ba mu son a zubar da jinin ko mutum ɗaya saboda kwaɗayin mulki.

“Ina amfanin baɗi ba rai. Mene ne alfanun kashe-kashe saboda mulki. Kuma wa ya san iyar waɗanda za su rasa rayukan na su. Idan kai ko ke ko ni muka rasa ran mu fa? Wa gari ya waya?” Inji Patience.

People are also reading