Home Back

Binciken El-Rufai: An Bayyana Dalilin Kafa Kwamitin Bin Diddigin Ayyukan Tsohon Gwamnan

legit.ng 2024/5/19

Jihar Kaduna - Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman, ya bayyana dalilin da ya sa majalisar ke binciken bashin da gwamnatin tsohon Gwamnan Jihar, Malam Nasir El-Rufai ta karɓo.

Liman ya faɗi dalilin ne a ranar Talata, 16 ga watan Afirilu, bayan da majalisar ta kafa wani kwamiti mai mutum 13 da zai yi bincike kan El-Rufai, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Dalilin bincikar El-Rufai
An kafa kwamitin binciken Nasir El-Rufai a Kaduna Hoto: Nasir El-Rufai Asali: Facebook

Kwamitin dai zai binciki lamuni, tallafi, da sauran ayyukan da aka aiwatar daga shekarar 2015 zuwa 2023 a lokacin El-Rufai.

Ya ba da tabbacin cewa za a duba lamarin yadda ya kamata, yana mai cewa za su ba kowa ƴancin faɗin gaskiya.

"Muna so ne kawai mu yi nazari kan yadda gwamnatin da ta shuɗe ta kashe kuɗaɗenta ta yadda za mu yi alfahari da kanmu zuwa lokacin da muka bar majalisa cewa mun yi abin da ya dace."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba mu son wani ya kira mu da ƴan amshin shata, ba mu yin wannan binciken domin aibanta wani, amma za mu yi abin da ya dace."

- Yusuf Liman

Asali: Legit.ng

People are also reading