Home Back

Matar Tinubu Ta Raba Milyoyi a Jihar Arewa, za a yi Rabo a dukkan Jihohi

legit.ng 2024/10/5
  • Matatar shugaban kasa, Oluremi Bola Ahmed Tinubu ta raba miliyoyin kudi ga mata a jihar Zamfara domin bunkasa ƙananan sana'o'i
  • An ruwaito cewa mata 1,000 ne suka samu kyautar tallafin a wannan karon yayin da matar shugaban kasar ta samu wakilci
  • Haka zalika matar shugaban kasar ta tabbatar da cewa za ta zagaya dukkan jihohin Najeriya domin raba kudin ga mata masu sana'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Matar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta ba mata tallafin kudi a jihar Zamfara.

An ruwaito cewa Oluremi Tinubu ta raba zunzurutun kudi har N50m ga mata domin bunkasa kananan sana'o'i.

Matar Tinubu
Oluremi Tinubu ta raba tallafi a Zamfara. Hoto: @HuriyyaDL Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa matar gwamnan jihar Zamfara ce ta wakilci Oluremi Tinubu yayin rabon kudin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar Tinubu ta raba N50m a Zamfara

Matar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta raba kudi N50,000 ga mata domin bunkasa sana'a a jihar Zamfara.

Tribune ta wallafa cewa mata guda 1,000 ne suka samu kyautar kuma kowace daya ta samu N50,000 inda kudin ya kai har N50m.

Dalilin raba milyoyi a Zamfara

Matar gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Hurriya Dauda Lawal ta ce an raba kudin ne domin a tallafi mata masu kananan sana'o'i.

Hajiya Hurriya ta ce ƙananan sana'o'i ne kashin bayan tattalin arziki saboda haka tallafa musu zai taimaka wa tattali.

Matar Tinubu za ta yi rabo a jihohi

Matar shugaban kasar ta bayyana cewa tallafin kudin na cikin kokarin da gwamnatin Tinubu take kuma za a zagaya dukkan jihohin Najeriya.

Oluremi Tinubu ta bayyana cewa a zuwa yanzu mata 70,000 ne suka ci moriyar shirin a fadin Najeriya.

An kaddamar da ba mata tallafi a Borno

A wani rahoton, kun ji cewa matar shugaban kasar Najeriya, Sanata Oluremi Bola Ahmed Tinubu, ta kaddamar da shirin ba da tallafi wa mata a jihar Borno.

Uwargidar Najeriyar ta samu wakilcin matar mataimakin shugaban kasa, Hajiya Nana Kashim Shettima yayin kaddamar da shirin a birnin Maiduguri.

Asali: Legit.ng