Matar Tinubu Ta Raba Milyoyi a Jihar Arewa, za a yi Rabo a dukkan Jihohi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - Matar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta ba mata tallafin kudi a jihar Zamfara.
An ruwaito cewa Oluremi Tinubu ta raba zunzurutun kudi har N50m ga mata domin bunkasa kananan sana'o'i.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa matar gwamnan jihar Zamfara ce ta wakilci Oluremi Tinubu yayin rabon kudin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta raba kudi N50,000 ga mata domin bunkasa sana'a a jihar Zamfara.
Tribune ta wallafa cewa mata guda 1,000 ne suka samu kyautar kuma kowace daya ta samu N50,000 inda kudin ya kai har N50m.
Matar gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Hurriya Dauda Lawal ta ce an raba kudin ne domin a tallafi mata masu kananan sana'o'i.
Hajiya Hurriya ta ce ƙananan sana'o'i ne kashin bayan tattalin arziki saboda haka tallafa musu zai taimaka wa tattali.
Matar shugaban kasar ta bayyana cewa tallafin kudin na cikin kokarin da gwamnatin Tinubu take kuma za a zagaya dukkan jihohin Najeriya.
Oluremi Tinubu ta bayyana cewa a zuwa yanzu mata 70,000 ne suka ci moriyar shirin a fadin Najeriya.
A wani rahoton, kun ji cewa matar shugaban kasar Najeriya, Sanata Oluremi Bola Ahmed Tinubu, ta kaddamar da shirin ba da tallafi wa mata a jihar Borno.
Uwargidar Najeriyar ta samu wakilcin matar mataimakin shugaban kasa, Hajiya Nana Kashim Shettima yayin kaddamar da shirin a birnin Maiduguri.
Asali: Legit.ng