Home Back

Sarakin Kano: Kotu Ta Soke Nadin da Aka Yi Wa Sanusi II? Ga Karin Haske Kan Hukuncin

legit.ng 2024/7/3
  • Kai tsaye, babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ba ta tsige Muhammadu Sanusi II daga kujerar sarkin Kano ba
  • Mai shari’a Abdullahi Liman ya ce dokar masarautar Kano ta 2024 wadda ta rusa masarautun jihar guda biyar na na daram
  • Sai dai alkalin ya yi fatali da matakan da gwamnan Kano, Abba Yusuf ya dauka wajen aiwatar da dokar rusa masarautun

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta bayyana cewa dokar masarautar Kano ta 2024 wadda ta rusa masarautun jihar guda biyar na na daram.

Amma kotun ta yi fatali da duk wani mataki da gwamnan Kano, Abba Yusuf ya dauka wajen aiwatar da dokar rusa masarautun jihar.

Kotu ta yi hukunci kan dokar masarautar Kano ta 2024
Kotu ta yi fatali da matakan da gwamnan Kano ya dauka wajen aiwatar da dokar rusa masarautu. Hoto: @masarautarkano, @AKabirbayero Asali: Facebook

Kotu ta soki matakan gwamnan Kano

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Mai shari’a Abdullahi Liman ya ce Gwamna Abba Yusuf ya yi biris da umarnin hana mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II kan kujerar sarki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari’a Abdullahi Liman ya ce duk da mai girma Abba bai karbi takardar umarnin a hannu ba, amma shi (gwamnan) ya amince cewa yana sane da umarnin.

Alkalin kotun ya ce ba daidai ba ne ba gwamnan ya yi watsi da bayanan umarnin kotun wanda aka yada a shafukan sada zumunta.

Abin da hukuncin kotun ya kunsa

1. Kotu ta ji koken majalisar Kano

Kamar yadda babban mataimaki na musamman ga gwamnan Kano a kan sabbin kafofin watsa labarai, Hassan Sani Tukur ya wallafa a X, kotun ta karbi bukatar majalisar Kano.

Kotun ta karbi korafin majalisar da na Antoni Janar na Kano kan dakatar da bukatar rusa dokar da majalisar ta zartar na sabunta dokar masarautun jihar.

2. Dokar da ta rusa masarautu na nan

Dokar masarautar Kano ta 2024, wacce ta rusa masarautun jihar guda biyar ta na nan amma kotu ta yi fatali da dukkanin matakan da gwamnan ya dauka na aiwatar.

3. Sauya kotun da za ta saurari shari'ar

Mai shari'a ya ba majalisa da gwamnatin jihar damar ci gaba da shari’ar kuma ya mayar da karar zuwa kotun Amobeda saboda karin matsayi da ya samu zuwa kotun daukaka kara.

Kotu ta soke nadin Sanusi II?

Bisa ga wannan hukunci da kotun ta yanke, har yanzu Muhammadu Sanusi II ne sarkin Kano har zuwa lokacin da kotun Amobeda za ta kammala sauraron shari'ar.

Kuma ko da kotun ta rusa nadin da aka yi wa Sanusi II, ko kuma ta tabbatar da nadin nasa, bangaren da suka sha kasa na iya kai shari'ar gaba zuwa kotun daukaka kara.

Kotu ta hana a wulakanta Sanusi II

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar kotun jihar Kano ta hana jami'an tsaro na ƴan sanda, sojoji da sauran jami'an tsaro fitar da Muhammadu Sanusi II daga cikin fadar sarki.

Kotun ta kuma hana jami'an tsaron yin duk wani abu da zai wulakanta Sanusi II har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan ƙarar da sarkin da masu nadin sarki suka shigar.

Asali: Legit.ng

People are also reading