Home Back

'Ba za mu yi abin da zai cutar da addini da al'adar Najeriya ba'

bbc.com 2024/10/4
..

Asalin hoton, X/Malaga

Ministan watsa labaran Najeriya, Alhaji Muhammad Idris Malaga ya shaida wa BBC cewa da babu ƙanshin gaskiya dangane da ruɗanin da ake yaɗawa cewa yarjejeniyar da gwamnatin Najeriya ta rattaɓa wa hannu na da alaƙa da ƴancin masu luwaɗi da maɗigo.

"...wannan al'amari ba haka yake ba..sai da aka kafa kwamiti. Sai da aka tantance babu wani abu ya da ya saba wa ko dokar Najeriya ko zamantakewarmu ba. Babu yadda za a yi gwamnatin Tinubu da Shettima ta yi abin da zai ci karo da dokokin Najeriya da abin da zai saɓa addini ko al'adun al'ummar ƙasarmu ba..." In ji ministan.

Shi ma ɗaya daga cikin masu taimaka wa shugaba Tinubu na Najeriya, Temitope Ajayi ya ce labarin da ke yawo cewa an rattaɓa hannu kan yarjejeniyar ne domin samun dala biliyan 150 domin bai wa masu neman jinsi guda damar yin dabdala, ana yi ne domin yaudarar jama'a.

Mai magana da yawun ministan tsare-tsare na kasar, Bolaji Adebiyi ya ƙara haske cewa "abin dariya ne da ɗan adam ba zai taɓa yin tunaninsa ba a ce gwamnatin Najeriya ta rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya domin bai wa masu neman jinsi guda damar yin abin da suke so a kan kuɗi dala biliyan 150..."

Binciken BBC

BBC ta samu kwafin yarjejeniyar ta Samoa mai shafi 172 daga Tarayyar Turai kuma bisa abin da kafar ta gani babu batun auren jinsi guda da batun kuɗi dala biliyan 150 da ake magana a kai a takardar sai dai kuma idan wani kwafin daban Najeriya ta rattaɓa wa hannu.

To sai dai kuma yarjejeniyar ta yi ƙarin haske kan amincewa wajen kawo ƙarshen nuna banbanci da cin zarafin mutane saboda irin abin da suka yi imani da shi ta fuskar jima'i.

Kuma ana sa ran dukkannin ƙasashen ƙungiyar ta OACPN za su yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen kawo ƙarshensu.

Mece ce yarjejeniyar Samoa?

..

Asalin hoton, PRESIDENCY/X

Samoa wata yarjejeniyar ce da ƙasashen Tarayyar Turai guda 27 suka yi da ƙasashen ƙungiyararayyar Afirka da Karebia da yankin Pacific, OACPS kimanin 79.

Yarjejeniyar kuma ta samo sunanta daga birnin Samoa na tsibirin Apia inda a nan aka ƙulla yarjejeniyar a ranar 15 ga watan Nuwamban 2023.

Abubuwan da yarjejeniyar ta ƙunsa sun haɗa da ƴancin ɗan'adam da batutuwan jima'i da dimokraɗiyya da jagoranci na gari da daidaito tsakanin jinsi. Sauran abubuwan da yarjejeniyar ta ƙunsa sun haɗa da samar da muhalli mai inganci da magance matsalar sauyin yanayi da dai sauransu.

Ana dai sa ran cewar yarjejeniyar ta Samoa za ta taimaka wa ƙasashe mambobi da suka rattaɓa hannu kanta, wajen haɓaka tattalin arziki ta hanyar sanya jari da alaƙar kasuwanci da cigaba da kuma zaman lafiya.

Sakatare Janar, na ƙungiyar ƙasashen Afirka da Karebiya da yankin Pacific, OACPS, Georges Rebelo Pinto Chikoti ya bayyana muradan yarjejeniyar da haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen samar da cigaba na haƙiƙa.

Me ƴan Najeriya ke cewa?

Batun yarjejeniyar Samoa da gwamnatin Najeriya ta rattaɓa wa hannu na ci gaba da haifar da ce-ce-ku-ce a ƙasar, inda ƴan kasar da dama suka hau kafafen sada zumunta domin sukar al'amrin bisa cewa rattaɓa hannun ya saɓa wa dokokin ƙasar.

Masu suka dai na cewa matsin lamba ce ta sa Najeriya ta amince da yarjejeniyar - inda suke zargin cewa tana ƙunshe da wani bangare da ya tilasta wa ƙasar nuna goyon baya ga masu neman jinsi kafin ta samu tallafin da ke ƙarƙashin yarjejeniyar, wani abin da ya saɓa wa dokar Najeriya.

Kauce wa Twitter, 1
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

Wannan yana cewa ku karanta yarjejeniyar mai warƙa 12 za ku fahimci ba wai Najeriya kaɗai ba har da sauran ƙasashe na nuna damuwa dangane da abubuwan da na ja wa layi..

Kauce wa Twitter, 2
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 2

Shi ma Mahadi Shehu ya tofa albarkacin bakinsu ta hanyar yin addu'a cewa " Muna addu'ar luwaɗi da maɗigo da cin zarafin yara su tabbata a halayyar ƴaƴansu, muna addu'ar abin ya bi jinin jikokinsu da jikokin-jikokinsu da tattaɓa kunnensu. Allah ya sa su mutu suna aikata halayyar."

Kauce wa Twitter, 3
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 3

Kauce wa Twitter, 4
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 4

Kauce wa Twitter, 5
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 5

Kauce wa Twitter, 6
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 6

Baya ga kafafen sada zumunta, batun na ci gaba da zama abin tattaunawa a kasuwanni da wuraren hirar jama'a.

Bayanai sun nuna cewa batun yarjejeniyar ta Samoa ne ya kankane mafi yawancin hudubobin sallar Juma'ar nan a garuruwa da biranen Musulmi a arewacin Najeriya.

Masu lura da al'amura dai na alaƙanta ce-ce-ku-cen da yarjejeniyar ta haddasa da gazawar jami'an gwamnati na yi wa ƴan Najeriya bayani kafin rattaɓa hannu kan yarjejeniyar ta Samoa.

Wasu ma na cewa ya kamata a ce an kai batun majalisar dokokin ƙasar domin neman sahhalewarta kafin rattaɓa hannu a wannan yarjejeniya.

People are also reading