Tuhumar Wulaƙanta Naira: Kotu Ta Ɗauki Mataki Kan Fitaccen Ɗan Kasuwa, Obi Cubana
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Legas - Wata babbar kotun tarayya da ke da zama a Legas ta umarci fitaccen ɗan kasuwa, Cubana Chief Priest ya biya gwamnati tarar N10m saboda tuhumarsa da wulaƙanta Naira.
Wannan na daga cikin yarjejeniyar da hukumar EFCC da ɗan kasuwar suka cimmawa a bayan fage, wanda Mai shari'a Kehinde Ogundare ya amince da ita.
A yayin zaman kotun na yau Talata, lauyar EFCC, Bilkisu Buhari-Bala ta shaidawa kotun cewa EFCC da Cubana sun daidaita a wajen kotu, in ji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan wanda ake kara, Chikaosolu Ojukwu (SAN) ya yabawa kokarin hukumar EFCC na warware matsalar cikin lalama kuma a karamin lokaci.
Mista Ojukwu ya ce wanda ya ke karewa ya yi nadamar abin da ya aikata kuma ya sha alwashin hakan ba zata sake faruwa a nan gaba ba.
Lauyan ya kuma nemi kotun da ta rushe tuhumar da ake yi wa Cubana Chief Priest, tun da dama manufar yin yarjejeniyar kenan.
Jaridar The Nation ta ruwai Mai shari'a Ogundare a hukuncin da ya yanke, ya amince da yarjejeniyar da Cubana da EFCC suka kulla, kuma ya soke tuhumar.
Kulla irin wannan yarjejeniyar na kunshe ne a cikin sashe na 14 (2) na dokar da ta samar da hukumar EFCC da aka kafa a 2004.
Dokar ce ta nemi wanda ake zargin ya biya gwamnatin tarayya tarar Naira miliyan 10, tare da kuma yin alkawarin gujewa faruwar laifin a gaba.
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya gargadi gwamnoni jihohi daga taba masarautun gargajiya.
Atiku Abubakar ya yi kira ga gwamnatin tarayya da 'yan majalisun tarayya da su yi garambawul ga kundin tsarin mulkin Najeriya domin ba da damar sanya masarautun gargajiya a cikin doka.
Asali: Legit.ng