Home Back

Ana fargabar rasuwar wani mutum sanadiyyar yi masa yankan Rago a sabon titin Panshekara da ke Kano.

dalafmkano.com 2024/5/17

A daren jiya Juma’a ne aka yi zargin wasu matasa da ba’a san ko su waye ba suka yiwa wani mutum yankan Rago, a yankin Sabon titin Panshekara da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar Kano.

A zantawar gidan rediyon Dala FM Kano, da wani ɗan kasuwa a yankin Sabon titin, ya ce lamarin ya faru ne bayan ƙarfe goma na daren jiya Juma’a, inda wasu rukunin matasa suka je yakin a cikin baburin Adai-dai Sahu riƙe da muggan makamai, yayin da suka ƙaddamar wa mutumin a kan titin ring road, daura da wajen siyar da gas ɗin Girki, wanda aka zargi dama matasan sun shiryawa abin.

Ɗan kasuwar ya ƙara da cewa, ana kyautata zaton matasan sun yiwa mutumin yankan Rago, bayan da ake zargin hakan yayi sanadiyyar rasuwar sa, kuma matasan suka tsere ba tare da an kama su ba.

Sai dai kawo yanzu rundunar ƴan sandan jihar Kano, bata ce komai ba akan al’amari, da zarar mun ji daga kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, zaku ji mu da shi akan batun.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da wasu fusatattun matasa suka addabi yankin Ɗorayi da Chiranchi, har zuwa Sabbin titin Panshekara, wajen ƙaddamar wa mutane da sara, tare da ƙwacen wayoyi, da kayan mutane, lamarin da yake sanya al’ummar yankin a cikin furgici da tashin hankali.

Ko da dai a yammacin ranar Laraba Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano CP Muhammad Usaini Gumel, ya yi wani zama da masu ruwa da tsaki a yankin na Ɗorayi ƙarama, domin lalubo hanyoyin magance matsalar tsaron, bisa yadda matasan suka addabi mutanen yankin, har ma ya ƙaddamar da ofishin ƴan sandan Anty Daba a Dorayin.

People are also reading