Home Back

Sanata Yari Ya Zaftare Kudin Takin Motoci 76 Da Kashi 50 Ga Manoman Zamfara

leadership.ng 2024/6/28
Sanata Yari Ya Zaftare Kudin Takin Motoci 76 Da Kashi 50 Ga Manoman Zamfara

Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, ya samar da manyan motocin takin zamani 76 da za a raba su ga manoma tare sa zaftare kashi 50 cikin 100 na farashinsa a matsayin tallafi. 

Ibrahim Muhammad, shugaban kwamitin yada labaransa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a Gusau ranar Talata.

A cewar sanarwar, shugaban kwamitin, Alhaji Lawal Liman ne, ya bayyana hakan a wani taro da mambobin kwamitin rabon takin.

Ya bayyana cewa, kowane daga cikin kananan hukumomi takwas na gundumar Zamfara ta Tsakiya da Arewa za su karbi manyan motocin takin guda biyar.

Sanarwar ta ce yankuna shida na gundumar Zamfara ta Yamma da Sanatan ke wakilta, kowanensu zai karbi manyan motocin takin zamani shida.

Liman ya ce ana sayar da takin tsakanin Naira 40,000 zuwa Naira 45,000 a kasuwa kan kowane buhu mai nauyin kilogiram 50, amma za su sayar wa manoma kan kudi Naira 20,000 kan kowane buhu.

Ya ce manufar tallafin shi ne ceto manoma a fadin jihar daga karancin taki da kuma rage hauhawar farashinsa.

Ya ce tallafin na da nufin zagaya wa mazabu 147 da ke kananan hukumomin jihar 14 ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.

Ya bukaci mambobin kwamitin rabon da su tabbatar da bin ka’ida wajen rabon takin.

Shugaban ya kuma sanar da cewa Sanata Yari, ya samar da manyan motoci 28 na shinkafa don raba wa mutane a fadin jihar a lokacin bikin sallah.

Ya ce tallafin zai shafi marasa galihu a fadin jihar.

“A karkashin tsarin da kwamitin malamai zai kula da shi wanda ya gudanar da ayyukan Sanatan a baya, an ware wa kowace karamar hukuma manyan motoci biyu na buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50,”.

Ya sake jaddada kudurin tsohon gwamnan wajen bayar da taimako ga al’ummar Jihar Zamfara.

Ya roki wadanda da aka bai wa amanar rabon kayan tallafin, da su rike amana su yi aiki da gaskiya.

People are also reading