Home Back

Spain Ta Kori Masu Masaukin Baki Jamus Daga Gasar EURO

leadership.ng 2024/8/23
Spain Ta Kori Masu Masaukin Baki Jamus Daga Gasar EURO

Kasar Spain ta kori masu masaukin baki daga gasar kofin kasashen Turai da ake bugawa a kasar Jamus,wasan wanda suka buga a filin wasa na Mercedez Benz ya tashi da ci 1-1 wanda hakan ya sa aka kara mintuna 30.

A minti na 51 da fara wasan Dani Olmo ya jefa kwallo a ragar Jamus kafin Florian Wiltz ya farke a minti na 89 bayan ya amshi kwallo daga hannun Joshua Kimmich kafin ya cilla wa mai tsaron ragar Spain Unai Simon.

Bayan karin mintuna 30 da alkalin wasa Anthony Taylor ya yi,wasan ya kara zafafa a wajen dukkanin kasashen biyu.

Mikel Merino ya raba gardama a wasan na yau bayan ya jefa kwallo ta biyu ga kasar Spain a minti na 119.

People are also reading