Home Back

An Dakatar Da Bellingham Daga Buga Wasanni Biyu Na Laliga Sakamakon Rikici Da Alkalin Wasa

leadership.ng 2024/4/29
An Dakatar Da Bellingham Daga Buga Wasanni Biyu Na Laliga Sakamakon Rikici Da Alkalin Wasa

An dakatar da dan wasan Real Madrid Jude Bellingham wasanni biyu a gasar LaLiga saboda jan katin da ya samu a wasan da suka tashi 2-2 da Kungiyar kwallon kafa ta Valencia.

Bellingham, mai shekara 20, ya yi tunanin ya zura kwallo a ragar Valencia kafin alkalin wasa, Gil Manzano ya soke kwallo sakamakon busa tashi da yayi kafin Bellingham ya ci kwallon a filin wasa na Mestalla ranar Asabar.

Hukumar kwallon kafa ta Spain (RFEF) ta ce Bellingham ya nuna halin raini ga Manzano lokacin da ‘yan wasan Real da ma’aikatansu suka kewaye shi,an kuma ci Bellingham, tarar Yuro 600 (£513).

Real ta daukaka kara kan jan katin da aka bai wa Bellingham amma kwamitin ladabtarwa na RFEF ya yi watsi da hujjarsu cewa alkalin wasa ya yi kuskure.

Real ta ba da tazarar maki bakwai a saman teburin LaLiga, inda Girona da Barcelona ke bin su a baya bayan buga wasan mako na 28.

 
People are also reading