Home Back

Kano: Masallata Sun Rasa Ransu Bayan Tirela Ta Bi Kansu Ana Tsaka da Jam'in Juma'a

legit.ng 4 days ago
  • An shiga wani irin yanayi bayan wasu masallata sun rasa ransu suna tsaka da sallah a masallacin Juma'a bayan tirela ta hau kansu
  • Lamarin ya faru ne a garin Imawa da ke karamar hukumar Kura a jihar Kano a yau Juma'a 28 ga watan Yunin 2024
  • Hukumar kiyaye hadura ta kasa, FRSC ita ta tabbatar da haka inda ta ce akalla mutane 14 sun mutu sanadin hatsarin motar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Hukumar kiyaye haduara ta kasa, FRSC ta tabbatar da mutuwar masallata akalla 14 a jihar Kano.

Hukumar ta tabbatar da cewa masallatan sun rasa ransu bayan tirela ta kutsa cikin jam'i a masallacin Juma'a.

Wasu masallata 14 sun rasu bayan tirela ta bi kansu a Kano
Babbar mota ta hallaka wasu masallata 14 yayin sallar Juma'a a Kano. Asali: Original

A ina iftila'in ya faru a Kano?

Lamarin ya faru ne a garin Imawa da ke karamar hukumar Kura kan hanyar Kano zuwa Kaduna da misalin karfe 1:30 na rana, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

FRSC ta tabbatar da cewa direban ya gagara shawo kan motar inda ya kutsa kan jama'a a yau Juma'a 28 ga watan Yunin 2024.

Kakakin rundunar reshen jihar Kano, Abdullahi Labaran ya ce an binne tara daga cikin wadanda suka rasu a yau Juma'a da rana.

Kano: Ana ci gaba da basu kulawa

Labaran ya ce sauran wadanda suka samu raunuka kuma suna ci gaba da karbar kulawa a asibiti.

Ya kara da cewa yanzu haka direban ya gudu ba a san ina yake ba inda ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu.

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading