Home Back

Rashin Osimhen A Cikin Tawagar Nijeriya Babbar Asarace – Samson Siasia

leadership.ng 2024/7/5

Tsohon Kocin Super Eagles, Samson Siasia, ya ce rashin Victor Osimhen zai iya shafar damar tawagar na samun sakamako mai kyau a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Duniya na FIFA 2026 da za su yi da Afirka ta Kudu da Jamhuriyar Benin.

An cire sunan Osimhen daga cikin ƴan wasan da zasu buga wasannin biyu masu mahimmanci saboda raunin da ya samu a ƙafarsa.

Siasia yace rashin ɗan wasan na Napoli zai saka abubuwa su zamo masu wahala ga Super Eagle kamar yadda jaridar SCORE Nigeria ta ruwaito.

Super Eagles dai ba ta samu nasara ba a rukunin C, kuma dole ne ta doke Afirka ta Kudu da Jamhuriyar Benin domin su dawo da martabarsu a cikin rukunin na C.

A ranar Juma’a ne tawagar Super Eagles ta Nijeriya za su kara da Bafana Bafana a birnin Uyo sannan su tafi Abidjan don karawa da Squirrels kwanaki uku bayan haka.

People are also reading