Home Back

Sanata Ndume, ya soki ingancin gyaran naira biliyan 42 da ake yi wa zauren majalisar dattawa

premiumtimesng.com 2024/5/20
Sanata Ndume, ya soki ingancin gyaran naira biliyan 42 da ake yi wa zauren majalisar dattawa

Sanata Ndume, dan majalisar dattawa mai wakiltar Borno ta Kudu, ya soki gyarar da aka yi wa majalisar dattawa wanda ya ce duk da an kashe naira biliyan 42, a ganinsa ‘Kwalliya ba ta biya kudin Sabulu ba.

Sanatan ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisar a ranar Talata.

Sanata Ndume ya ce duk da makudan kudin da aka kashe har naira biliyan 42, zauran majalisar bata yi kama da zauren majalisa ba, wurin ya yi kamar dakin taro.

“Wannan ba zauren majalisa bane, abu kamar dakin taro. Kamar yadda nake magana yanzu ba za ku ma gane ko nine Ndume ke magana ba saboda shirmen na’urar saurare da yin magana da aka sassaka.

Sanatan ya lura cewa tsarin zama da kuma gyara kujeru a zauren da aka yi wa kwaskwarima shima yana bukatar gyara.

“Muna bukatar gyara wannan. Muna bukatar mu canja abubuwa da yawa.

Sannan kuma ya ce hatta na’urar yin zabe kai tsaye da za a rika gani ma wanda a zauren a kwai yanzu babu.

Ba a saka agogon bango na kirki ba, kuma wai an kashe naira biliyan 42.

Da yake jawabi bayan korafin Ndume, Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya ce wannan aiki sai dai a tuhuma majalisar da ta shude, wato majalisar da Ahmed Lawan ya shugabanta.

” Majalisar baya ce ta ba da kwangilar gyra zauren majalisar, ba mu ba saboda haka sune suka yi shirme. Amma kuma za duba abinda ya dace ayi a gyara.

People are also reading